Ana Tsaka da Cece-Kuce Kan Mayar da Manyan Ofisoshi Legas, Tinubu Zai Lula Kasar Faransa

Ana Tsaka da Cece-Kuce Kan Mayar da Manyan Ofisoshi Legas, Tinubu Zai Lula Kasar Faransa

  • Jirgin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa birnin Faris, kasar Faransa a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu
  • Ana kuma sa ran Tinubu zai dawo gida Najeriya a farkon watan Fabrairu mai kamawa bayan ya kammala abubuwan da suka kai shi na gashin kai
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yan Najeriya musamman daga yankin arewa suka nuna adawa da yunkurin gwamnatinsa na mayar da manyan ofisoshi Legas daga Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fadar shugaban kasa, Abuja - Rahotanni dake zuwa sun tabbatar da cewar jirgin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai shilla birnin Faris, kasar Faransa.

Wannan ziyara da shugaban kasar zai kai kasar Faransan na gashin kai ne ba ziyarar aiki ba, kamar yadda rahoton ya nuna.

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da Legas babban birnin Najeriya? Fadar shugaban kasa ta fayyace gaskiya

Tinubu zai shilla kasar Faransa
Ana Tsaka da Cece-Kuce Kan Mayar da Manyan Ofisoshi Legas, Tinubu Zai Lula Kasar Faransa Hoto: The Presidency
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun, ne ya tabbatar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na X a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"A yau ne Shugaban kasa Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Faris, kasar Faransa domin wata ziyarar gashin kai, zai dawo kasar ne a makon farko na watan Fabrairu, 2024."

Tinubu zai shilla Faransa ana tsaka da sukar shirin gwamnatinsa

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan shirin da gwamnatin Tinubu ke yi na dauke wasu manyan ofisoshi daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Legas.

Mun dai ji cewa kungiyar ACF ta Dattawan Arewa ta soki shirin dauke hedikwatar hukumar FAAN daga birnin tarayya zuwa Legas.

Haka kuma, kungiyar ba ta goyon bayan a dauke wasu manyan ofisoshin babban bankin CBN daga Abuja.

Kara karanta wannan

Jajirtaccen Sanatan Arewa ya fadi masu kai Shugaban kasa su baro shi a Aso Villa

Har ila yau, sanatocin Arewa sun nuna rashin amanna da dauke wadannan ofisoshi da za ayi daga birnin tarayya zuwa garin Legas.

Ndume ya soki manufar gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya soki dauke wasu ofisoshin gwamnati daga Abuja.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya yi hira da tashar Channels a kan shirin maida wasu ofisoshin CBN da hedikwatar FAAN zuwa Legas.

Babban ‘dan siyasar ya yi ikirarin wasu miyagun ‘yan siyasa suke fadawa Mai girma shugaban kasa karya wajen daukar matakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng