Wani Mutumi Ya Mutu Bayan Gama Sharholiya da Budurwarsa a Otal
- Wani mutumi ya ce ga garin ku nan bayan ya kammala goge raini a kan gado a ɗakin otal tsakaninsa da wata mata a jihar Ondo
- Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ta yi caraf da mutum biyu da ake zargi
- Matar da mutumin ya sheƙe ayarsa da ita da manajan otal ɗin dai su ne mutanen da ƴan sandan suka yi caraf da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Rundunar ƴan sandan jihar Ondo a ranar Talata ta ce ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da kashe wani mutum, mai suna Abiodun Akintomowo, a garin Ondo na jihar Ondo.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Akintomowo ya rasa ransa ne bayan da ya yi lalata da wata mata da ake zargin budurwarsa ce a wani otal da ke unguwar Akinjagunla, a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, wacce ta ƙi bayyana sunayen waɗanda ake zargin, ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin budurwa ce ga marigayin, yayin da wanda ake zargi na biyu shi ne mai otal ɗin da lamarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamanta:
"Mutumin (marigayin) bai ji daɗi ba bayan gama jima’i da matar a otal, don haka aka garzaya da shi asibiti daga baya ya mutu. Har yanzu mutanen biyu suna hannunmu."
Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin yayin da aka ajiye gawar mutumin a ɗakin ajiye gawa na wani asibiti a garin.
Yadda lamarin ya auku
Wata majiya ta ce matar ta sanar da halin da ake ciki ne lokacin da marigayin ya faɗi a ɗakin otal ɗin bayan sun gama sharholiyarsu, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.
A cewar majiyar:
"Matar ta sanar bayan da ta fahimci cewa mutumin ya faɗi, manajan otal ɗin da wasu mutane sun yi tururuwa zuwa wurin da lamarin tare da ƙoƙarin ceto shi. Daga baya aka tabbatar da mutuwarsa."
Majiyar ya ƙara da cewa daga baya mahukuntan otal din sun kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda na Yaba da ke yankin.
Mata Ta Sheƙe Abokin Sharholiyarta
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mata ta shiga hannun ƴan sanda bayan ta halaka abokin harƙallarta a jihar Rivers.
Matar dai ta aikata wannan aika-aikar ne bayan marigayin ya buƙaci da su ƙara goge raini a kan gado.
Asali: Legit.ng