Allah ya kyauta: Wani mutumi ya mutu a daidai lokacin da yake lalata da budurwa a otel
- Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa an samu gawar wani magidanci a dakin otal a yankin Ibusa
- An gano cewa mutumin ya mutu ne bayan da ya kai karuwa otal din
- Karuwar ta tsere inda ta boye amma 'yan sandan sun cafkota don neman karin bayani
Rundunar 'yan sandan jihar Delta a ranar Juma'a sun tabbatar da mutuwar wani mutum a wani otal dake yankin Ibusa.
Kakakin 'yan sandan hukumar, DSP Onome Onovwakpoyeya ta sanar da manema labarai a garin Asaba cewa lamarin ya faru ne a Alhamis.
Tace hukumar otal din ne suka kai wa 'yan sandan yankin Ibusa din rahoto.
Onovwakpoyeya tace: "mun samu rahoton aukuwar lamarin kuma jami'anmu sun je inda abun ya faru tare da dauke gawar. A halin yanzu mun fara bincike a kan lamarin."
Majiyoyi sun bayyana cewa ana zargin mutumin ya mutu ne bayan ya dau karuwa wacce ya kwanta da ita.
KU KARANTA: Na aureshi a lokacin yana makaho, amma yanzu da ya fara gani yace zai sake ni saboda ni mummuna ce
Mamacin mai shekaru 55 har zuwa mutuwar shi direban mota ne.
"Mutumin yana da aure kuma yana zaune da iyalanshi a Ibusa. A ranar da abun ya faru, yaje otal din da wata mata mahaifiyar yara uku. "Matar ta fita daga dakin daga baya inda ta sanar da hukumar otal din da su duba mutumin don bashi da lafiya. A nan ne kuwa aka gano mutumin baya motsi wanda hakan yasa aka kira hukuma," daya daga cikin majiyar ta sanar.
Majiyar da ta nemi a sunanta ta bayyana cewa matar ta gudu bayan fita daga otal din amma 'yan sanda sun kama ta daga baya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng