DSS Ta Kama Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa, Dalili, Bayanai Sun Fito

DSS Ta Kama Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa, Dalili, Bayanai Sun Fito

  • Jami'an hukumar DSS da sojojin Najeriya sun kutsa ofishin kungiyar Miyetti Allah da ke Nasarawa, sun yi awon gaba da shuganta, Bodejo
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kama Bodejo ne biyo bayan kaddamar da wata kungiyar 'yan banga a jihar Nasarawa ba tare da izini ba
  • A cewar wata majiya daga hukumar DSS, ana fargabar wannan kungiyar da Bodejo ya kaddamar za ta haifar da tashin hankali a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Nasarawa - Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta kasa sun cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, kan kafa kungiyar ‘yan banga a Nasarawa.

An kama Bodejo ne a ranar Talata a babban ofishin Miyetti Allah, da ke kasuwar dabbobi ta Tundun Maliya a babban titin Abuja-Keffi, cikin Karamar hukumar Karu a Jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin APC ta kai karar Gwamnatin Tarayya kotu a kan tsohon bashin N138bn

DSS sun cafke Bodejo, shugaban Miyetti
DSS sun cafke Bodejo, shugaban Miyetti Allah saboda kafa kungiyar 'yan sa kai
Asali: Twitter

Rahoton The Punch ya nuna cewa jami’an DSS tare da wasu sojoji sun kai je ofishin Miyetti Allah da misalin karfe 3:40 na yammacin ranar Talata, inda suka kama Bodejo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa DSS ta kama Bodejo

Wata majiya ta DSS ta bayyana cewa an kama Bodejo ne saboda fargabar cewa kirkiro kungiyar ‘yan banga na Nomad’s na iya haifar da tashin hankali a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa kungiyar ba ta da rajista da DSS, ‘yan sanda, ko wata hukumar tsaro, don haka gwamnatin tarayya ba ta amince da ita ba, Leadership ta ruwaito.

Da aka tuntubi kakakin hukumar ta DSS, Dokta Peter Afunanya, bai amsa kiran waya da sakon tes da wakilin jaridar ya yi masa ba.

Miyetti Allah ta kaddamar da kungiyar 'yan banga a Nasarawa

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugabanta, ta fadi babban dalili 1

A ranar Alhamis da ta gabata ne muka kawo maku rahoton cewa kungiyar Miyetti Allah ta kaddamar da kungiyar 'yan sa kai mai suna 'Nomad Vigilante Nigeria'

Bodejo, shugaban kungiyar na kasa ya jaddada cewa kungiyar 'yan sa kan da suka kaddamar za ta bi dukkanin dokokin Najeriya wajen gudanar da ayyukan su.

A yayin kaddamar da kungiyar a Lafiya, jihar Nasarawa, Bodejo ya nemi mambobin kungiyar su yi aiki tare da 'yan sanda, sojoji da sauran jami'an tsaro don magance matsalar tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.