Mata da miji sunyi karyar yan bindiga sun sace su domin dangi su musu karo-karon naira miliyan 5

Mata da miji sunyi karyar yan bindiga sun sace su domin dangi su musu karo-karon naira miliyan 5

  • Yan sanda sun kama mata da miji da suka yi karyar an yi garkuwa da su don su samu kudin fansa har naira miliyan biyar
  • Hankulan iyalan ma'auratan ya tashi bayan da aka kira su a waya aka nemi kudin fansar, inda suka shigar da karar lamarin ga "yan sanda
  • Sai dai bayan tsananta bincike, jami'an tsaron sun gano ma'auratan, wadanda kuma suka amsa laifin su tare da fadin dalilin yin karyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu ma’aurata da ake zargi da yin garkuwa da kansu da nufin karbar kudin fansa har naira miliyan biyar.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna kan wani laifin da ya aikata lokacin yana ofis

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yayin da ya gargadi ‘yan kasar da su guji yin garkuwa da kansu.

An kama ma'aurata sun yi garkuwa da kansu
Yan sanda sun kama ma'aurata sun yi garkuwa da kansu, sun nemi N5m daga 'yan uwa. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Adejobi ya kara da cewa an kama wani mai suna Albarka Sukuya a jihar Filato da laifin yin garkuwa da kan shi a lokuta daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Guardian ta ruwaito cewa akwai kuma wani Nnamdi Agu, shi ma an kama shi da laifin yin karyar sace shi a Abuja da nufin damfarar iyalinsa.

Bayani game da wadanda aka kama sun yi garkuwa da kansu

Sanarwar ta ce:

“A Legas, kwanan nan aka kama wasu ma’aurata da laifin yin garkuwa da kansu da nufin karbar kudin fansa naira miliyan 5.
“Mijin sunan sa Doubara David Yabrifa, dan shekara 53 kuma ma’aikacin fasaha, da matar Regina Yabrifa, ‘yar shekara 48, mai gyaran jiki da gyaran kashi."

Kara karanta wannan

Me yasa kasar Saudiyya ke narka makudan kudade a harkar wasanni? An samu cikakken bayani

Sanarwar ta kara da ma’auratan sun amsa laifin shirya yin garkuwa da kansu domin tara naira miliyan 3 don siyan wani gida a Badagry da ke Legas, Vanguard ta ruwaito.

"Abun takaici ne yadda mutanen suke yin amfani da yanayin garkuwa da mutane da ake fama da shi yanzu wajen shirya garkuwa da kan su don samun kudi."

A cewar sanarwar.

Filato: An harbawa korararrun 'yan majalisu barkonon tshouwa

A wani labarin da ya faru a safiyar ranar Talata, 'yan majalisar PDP su 16 da Kotun Daukaka Kara ta kora a jihar Filato sun yi yunkurin kutsa kai cikin ginin majalisar jihar.

Sai dai jami'an 'yan sanda sun hana su wucewa, inda ta kai ga sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa korarrun 'yan majalisar da magoya bayan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.