Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Garkuwa da Iyalansa da Wasu Mutane 16 a Jihar Arewa
- Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari, sun kashe magajin gari tare da sace wasu sama da 10 a jihar Neja
- Shugaban ƙaramar hukumar Munya, Aminu Najume, ya ce ƴan ta'addan sun fito ne daga ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
- Wani mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa maharan sun kashe shugabansu, sun tafi da iyalansa da dama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - 'Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 16 a wani hari da suka kai kauyen Tsohon Dungunu da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
Da yake zantawa da jaridar The Cable ranar Litinin, Aminu Najume, shugaban karamar hukumar Munya, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Asabar.
Najume ya ce ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin gidan wani Alhaji Adamu, inda suka kashe shi tare da yi awon gaba da wasu daga cikin iyalansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Ba mutane 21 ne aka sace ba, mutum 16 ne aka yi garkuwa da su. Eh, an kashe Alhaji Ahmadu a harin wanda ya faru da misalin karfe biyu na safiyar ranar Asabar.
"Sun shigo nan yankin ne ta hanya Chikun, ƙaramar hukuma a Kaduna da ta haɗa iyaka da ƙaramar hukumar Munya a Neja. Sun tafi da mutum 16 kuma sun ɗauki wasu daga cikin iyalan wanda suka kashe.
"Mutum 3 kaɗai suka kyale daga cikin iyalan Alhaji Ahmadu bayan sun kashe shi, amma sun tafi da sauran gaba ɗaya."
Ƴan bindiga sun kashe basaraken ƙauyen
Yayin da yake tabbatar da harin, Dantala Noma, wani mazaunin kauyen, ya ce Ahmadu Mai Anguwa, wanda aka kashe shi ne Magajin Garin Tsohon Dunguna.
Noma ya ce kimanin mutane bakwai da ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su sun tsere daga hannunsu, sun koma gida.
Mutumin ya ce:
"Sun yi garkuwa da mutane 16 a kauyen, sun shiga gidan Mai Anguwa, sunansa Ahmadu Mai Anguwa, Magajin Garin mu, suka kashe shi, sannan suka tafi da iyalansa."
Duk wani yunƙirin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, bai kai ga nasara ba domin bai ɗaga kiran waya ko amsa saƙo.
'Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutanen Abuja
A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun saƙo karin mazauna birnin tarayya Abuja da suka yi garkuwa da su tun ranar Lahadin da ta wuce.
Tun farko mahara sun yi awon gaba da mutum 10 yayin da suka kai hari Sagwari Estate a karamar hukumar Bwari, sun kashe 3 daga ciki.
Asali: Legit.ng