Kano: Yayin da Rashin Tsaro Ya Addabi Arewa Maso Yamma, Yan Sanda Sun Dauki Muhimmin Mataki a Jihar
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kara tsaurara tsaro don tabbatar da kare al’ummar jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da rashin tsaro ke kara kamari a yankin Arewa maso Yammacin kasar
- Kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka a yau Lahadi 21 ga watan Janairu a Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Yayin da ake fama da matsalar tsaro a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, ‘yan sanda a Kano sun dauki mataki.
Rundunar ‘yan sanda a jihar sun kara yawan jami’ansu da ke sintiri musamman a bakin iyakokin jihar gaba daya, cewar Punch.
Wani mataki 'yan sanda suka dauka a Kano?
Wannan na zuwa ne yayin da sauran jihohin Arewa maso Yamma ke fama matsalar tsaro musamman garkuwa da mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar a jihar, shi ya bayyana haka a yau Lahadi 21 ga watan Janairu a Kano, cewar DayBreak Nigeria.
Kiyawa ya ce sun zuba jami’ansu a kan manyan hanyoyin da suka hada jihar da suka hada da Bauchi da Kaduna da Katsina.
Ya ce sun baza jami’ansu a dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa don tsaurara tsaro wacce ta hada iyaka da jihohin Kaduna da Plateau, cewar NewsNow.
Idan ba a mantaba, dajin Falgore ya kasance maboyar ‘yan bindiga da masu satar shanu da ma dukkan masu aikata laifuka.
Martanin rundunar kan matsalar
Ya ce:
“Mun baza jami’anmu zuwa dajin Falgore da ya hada iyaka da jihar Kaduna don dakile ‘yan ta’adda da ke shigowa daga Kaduna.
“Duk da jihar Kano ba ta fuskantar matsalar tsaro, amma ba za mu gajiya ba don tabbatar da jihar ta kasance cikin aminci.”
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya ba da umarni ga dukkan jami'ansu a kananan hukumomi 44 su kara himma a wuraren binciken ababan hawa.
‘Yan sanda sun fitar da rahoto a Kano
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta fitar da rahoton laifuka bayan hukuncin Kotun Koli.
Rundunar ta sanar da cewa ba a samu aikata wani laifi ba a jihar duk da tsammanin rashin tsaro da aka yi.
Asali: Legit.ng