Wata Mata Ta Sheke Abokin 'Sharholiyarta' Bayan Da Ya Nemi Karin Lalata Da Ita

Wata Mata Ta Sheke Abokin 'Sharholiyarta' Bayan Da Ya Nemi Karin Lalata Da Ita

  • Wani magidanci mai suna Igbodike Anthony, ya mutu a hannun wata mata bayan ta daba masa wuka a garin Fatakwal na jihar Rivers
  • An tattaro cewa, Sarah Nwankpo ta daba wa Igbodike wuka har lahira ne saboda abokin harkallarta ya nemi karin gamsuwar jima'i daga gare ta a ranar 22 ga Disamba, 2023
  • Mazaunan yankin ne suka yi nasarar kulle Sarah a lokacin da take kokarin tserewa daga gidan mamacin da ta kwanta dashi a ranar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Port Harcourt, jihar Rivers - An kama wata mata mai suna Sarah Nwankpo mai shekaru 26 da haihuwa da laifin kashe abokin harkallarta, Igbodike Anthony a garin Fatakwal na jihar Rivers.

Kara karanta wannan

An kama wani matashi da ya kware wurin satar kayan coci, za a gurfanar da shi

A cewar Vanguard, Sarah ta sirace ne daga gidan saurayinta, Joe Ibanga zuwa gidan marigayin a ranar 22 ga Disamba, 2023, inda lamarin ya faru, Vanguard ta ruwaito.

Sarah ta bayyana cewa ta hadu da Igbodike ne a 2017 lokacin da take zaune a Enugu kafin ta koma Fatakwal a watan Agustan 2023.

'Yan sanda sun kame matar da kashe abokin fajircinta
An kama matar da ta kashe abokin fajircinta | Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda suka hadu da juna

Ta ce marigayin yakan gayyace ta ta zo gidansa, wani lokacin kuma ya aika mata da kudin sufuri don ta zo su aikata abin da za su aikata.

A karshe dai ta ziyarce shi kuma ta yi lalata da shi a ranar 22 ga Disamba, 2023, bayan ya sake kira ya gayyace ta don zuwa wurinsa, Within Nigeria ta tattaro.

Meye ya faru ta sheke shi?

Da take ba da labarin yadda abin takaicin ya faru, ta ce:

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta cinye tsohuwa mai shekaru 80 a jihar Benue

“Da ya gama cin abinci, sai ya ce na masa tausa. Na bi abin da ya fadi amma daga baya na daina lokacin da ya bukaci jima'i daga gare ni. Na ce masa ba ni da kwanciyar hankali yin hakan.
“Kin amincewa da na yi ya bata masa rai. Ya ce in shirya in bar gidansa. Lokacin karfe 10 na dare. Na ki fita na tsaya na kalubalance shi. Mun yi cacar baki.”

Mai gidan da suke ciki da ’yan uwansa nan take suka ankara a lokacin da Sarah ta yi kokarin tserewa daga gidan bayan ta aikata laifin kashe abokin fajircinta.

Mata ta kashe mijinta a Kudancin Najeriya

A wani labarin, wata Ramota Soliu ta halaka mijinta, Bello Soliu ta hanyar watsa masa tafasashshen ruwa a unguwar Fulani dake yankin Iyana Ilewo da ke karamar hukumar Abeokuta ta arewa da ke jihar.

Manema labarai sun tattaro bayanai akan yadda ta watsa wa Bello ruwan zafin wanda ya yi ajalinsa, Nigerian Tribune ta ruwaio.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.