Tashin Hankali Yayin da Wani 'Bam' Ya Tashi da Mutane a Jihar Arewa, Ya Tafka Mummunar Ɓarna

Tashin Hankali Yayin da Wani 'Bam' Ya Tashi da Mutane a Jihar Arewa, Ya Tafka Mummunar Ɓarna

  • Rahotanni sun bayyana cewa wani abu da ake zargin 'Bam' ne ya tashi a garin Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna
  • Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa a bayanan da ta samu daga jami'an tsaro, mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu 10 suka ji rauni
  • Malam Uba Sani ya yi ta'aziyya da addu'a ga waɗanda suka rasu kana yi wa marasa lafiya fatan farfaɗowa cikin sauri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu rahoto daga jami’an tsaro na cewa an samu fashewar wani abu a ƙauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa.

A rahoton da jaridar Vanguard da tattaro, fashewar ta yi ajalin ƙaramin yaro ɗaya tare jikkata mutane 10.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 16 a Kaduna

Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna.
Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar da Fashewar Wani Abu, Mutum Daya Ya Mutu Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Samuel Aruwan, kwamishinan da ke kula da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"A rahoton farko da aka tattara da ya fito daga sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro, wani almajiri a kauye ya ɗakko abun fashewar daga daji.
"Almajirin na karatu a karkashin wani malami, bayan ya ɗauko abun ya dawo cikin abokansa, kwatsam sai abun ya tashi. A yanzu almajiri ɗaya, Zaidu Usman, ya mutu yayin da wasu 10 suka ji rauni.
"Yanzu haka waɗanda suka ji rauni na kwance a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika, ana kula da lafiyarsu."

Gwamna Uba Sani ya aika sakon ta'aziyya

Sanarwan ta kara da cewa Gwamna Malam Uba Sani ya kaɗu da samun labarin faruwar lamarin, inda ya jajantawa iyalan waɗanda abun ya shafa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sako ƙarin mazauna Abuja da suka yi garkuwa da su, sun turo saƙo

Kwamishinan ya ce:

“Gwamna Uba Sani ya kadu da abinda ya auku, sannan ya mika sakon ta’aziyya ga wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya tashi kafaɗun masu jinya."

Gwamnan ya kuma yi kira ga iyaye da jagororin al’umma da su kara sanya ido kan ‘ya’yansu da waɗanda ke karkashinsu, duba da yadda zamani ya sauya a yanzu.

Ya kuma umarci ma'aikatar tsaro ta haɗa kai da hukumomin tsaro wajen binciko abin da ya haddasa lamarin, kana ta kai agajin gaggawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Channels tv ta ruwaito.

Makama Kidandan, mazaunin garin da lamarin ya auku ya tabbatar da faruwar lamarin ga Legit Hausa, inda ya ce almajiran sun ɗauko abun daga daji ba tare da sun san menene ba.

A kalamansa ya ce:

"Eh gaskiya ne a cikin garin Kidandan lamarin ya faru, yau kwana huɗu kenan almajiran sun je yo itace kamar yadda suka saba, suka tsinci bam ɗin a cikin gwangwani.

Kara karanta wannan

An tafka asarar miliyoyin naira bayan gobara ta tashi a wata fitacciyar kasuwa

"Ba su san menene a ciki ba suka ɗauko suka aje a ɗakin da suke kwana tsawon kwana uku. To lokacin suna kwance, sai wanda abun ke hannunsa ya ɗauko yana wasa.
"Yana cikin wasan ne ya sake shi a ƙasa, yana faɗuwa kawai ya tashi da su, ɗaya dai ya mutu a yanzu, sauran suna asibiti, muna fatan Allah ya kiyaye gaba."

Rikici ya yi ajalin mutane a Kogi

A wani rahoton na daban An rasa rayuka da dukiya mai dimbin yawa yayin rikicin kalibalanci ya ɓarke tsakanin mazauna kauyuka biyu a jihar Kogi.

Mamba mai wakiltar mazaɓar Ankpa 1, Honorabul Lawal ya tabbatar da lamarin tare da kira ga mahukunta su kai agajin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262