Matan da Suka Haifi ’Yan 2 Za Su Samu N50k, an Bayyana Abin Masu ’Yan 3 Za Su Samu Don Kula da Su

Matan da Suka Haifi ’Yan 2 Za Su Samu N50k, an Bayyana Abin Masu ’Yan 3 Za Su Samu Don Kula da Su

  • Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta kaddamar da wani shiri na tallafawa mata masu haihuwan 'yan biyu da 'yan uku
  • Mai dakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno ta bayyana kyautar kudade ga mata masu yawan haihuwa duk wata
  • Ta ce za a rinka ba da naira dubu 50 ga matan da suka haifi 'yan biyu yayin da aka ware dubu 100 ga wadanda suka haifi 'yan uku

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - Mai dakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno ta bayyana kyautar kudade ga mata masu yawan haihuwa.

Patience ta ce ta amince da biyan kudade naira dubu 50 ga matan da suka haifi 'yan biyu yayin da ware dubu 100 ga wadanda suka haifi 'yan uku.

Kara karanta wannan

An yi wa shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, fashi a Landan

Mata masu haihuwan 'ya'ya fiye da 1 za su caba a wata jihar Najeriya
Matan da Suka Haifi ’Yan 2 Za Su Samu N50k, Yayin da Masu 'Yan 3 Za Su Samu N100k. Hoto: Umo Eno.
Asali: Facebook

Mene gwamnatin Akwa Ibom ta yi?

Ta ce ta yi hakan ne don taimakawa matan da kuma rage musu nauyin kula da iyalansu, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan kaddamar da shirin tallafawa mata musamman wadanda suke haifar 'ya'ya fiye da daya.

Yayin da ta ke kaddamar da shirin a yankin Ikot Ekpene ta ce za a rinka biyan kudaden ne a ko wace wata.

Wane alkawari matar gwamnan ta dauka?

Ta ce:

"Kun ga yadda ikon Allah ya ke, hakan ya cancanci murna shiyasa da ni da ku muka taru a nan.
"Wadannan yara za su kawo muku albarka, saboda su za ku sanu, kuma mutane za su mutunta ku saboda wadannan yara da kuke dauke da su."

Da ya ke magana, shugaban karamar hukumar Ikot Ekpene, John Etim ya yabawa matar gwamnan saboda wannan tallafi.

Kara karanta wannan

Satar mutane a Abuja: "Mun kama wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri", Wike ya yi karin bayani

Etim ya ce wannan tallafi zai taimakawa gwamnatin Eno a matsayin wacce ta ke taba rayuwar mutane, cewar Daily Post.

An maka hadimin Buhari a kotu

A wani labarin, Hadimin tsohon shugaba,n Najeriya, Muhammadu Buhari, Sanata Ita Enang ya gurfana a gaban kotun kan zarginsa da ake yi.

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel shi ya maka Enang a gaban kotun kan kokarin bata masa suna a ko yaushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.