Hukumar NITT: Shugaba Tinubu Ya Sabonta Nadin Bayero Farah

Hukumar NITT: Shugaba Tinubu Ya Sabonta Nadin Bayero Farah

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Bayero Farah a matsayin shugaban Hukumar Koyar Da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT)
  • Farah zai shugabanci hukumar ne a karo na biyu, kuma nadin nasa ya fara aiki ne tun a ranar 13 ga watan Janairu
  • Nadin nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Dr Bayero Farah a matsayin shugaban Hukumar Koyar Da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT), ta Zaria.

Mai magana da yawun hukumar, Mista John Kolawale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Zaria, a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

Shugaba Tinubu ya yaba nada shugaban NIIT
Shugaban kasa Tinubu Ya Nada Bayero Farah a Matsayin Shugaban NITT Hoto: The Presidency
Asali: Facebook

Farah zai sake shugabantar hukumar a zango na biyu, kuma nadin nasa ya fara aiki ne tun a ranar 13 ga watan nan na Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

'Takardar amincewa da sake nadin nasa na dauke da saka hannun babban sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume."

A cewarsa, sake nadin nasa ya yi daidai da tanadin dokar hukumar fasahar sufuri ta Najeriya, ta 1986 dokokin Tarayyar Najeriya.

Ya ce Farah na da kwarewa wanda ya haifar da gagarumin canji da ba a taba ganin irinsa ba, tare da kai NIIT zuwa matsayin da ba a taba ganin irinsa ba tun kafuwarta a shekarar 1986, rahoton Blueprint.

Kolawale ya ce tun a shekarar 1994 shugaban cibiyar ya fara aiki a NITT a matsayin babban jami'in kula da ci gaban ma'aikata, bayan ya yi aiki a matsayin malamin makaranta sannan sga bisani a matsayin jami'in hukumar kidaya ta kasa.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo bayan Tinubu ya amince da manyan kudurori 3 da za su sauya rayuwar talaka a yau

Ya kai matsayin darakta a shekarar 2013 sannan kuma ya zama shugaban cibiyar a ranar 13 ga watan Janairu 2020.

Tinubu ya nada hadimar Buhari mukami

A wani labarin kuma, mun ji cewa rabon muƙaman gwamnati da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ke yi a yan kwanakin nan ya dira Benin City, babban birnin jihar Edo.

A wannan karon, Shugaba Tinubu ya naɗa Didi Esther Walson-Jack a matsayin babbar sakatariya a ma'aikatar ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng