Buhari ya tabbatar da Salih-Farah a matsayin Shugaban NITT

Buhari ya tabbatar da Salih-Farah a matsayin Shugaban NITT

- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Bayero Salih-Farah a matsayin Darakta-Janar kuma babban Shugaban makarantar fasahar sufuri

- Hakan na kunshe a cikin wata wasika dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma’aikatar sufuri ta tarayya, Sabiu Zakari

- Nadin wanda zai shafe tsawon shekaru hudu ya fara aiki ne daga ranar Litinin, 13 ga watan Janairu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Dr Bayero Salih-Farah a matsayin Darakta-Janar kuma babban Shugaban makarantar fasahar sufuri wato Nigerian Institute of Transport Technology (NITT) da ke Zari’a.

Daraktan harkokin labarai na NITT, Mista Paul Mashelizah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 21 ga watan Janairu a Zaria.

Masheliza ya ce nadin na kunshe a cikin wata wasika dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma’aikatar sufuri ta tarayya, Sabiu Zakari.

Ya ce nadin wanda zai shafe tsawon shekaru hudu ya fara aiki ne daga ranar Litinin, 13 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Da karfe 2 na rana Kotun koli za ta yanke hukunci kan zabukan gwamnan Adamawa da Benue

Salih-Farah wanda aka Haifa a ranar 11 ga watan Maris 1964 a Kagoro, karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna ya mallaki digiri a fannin sanin yanayin kasa a 1987 daga jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto.

Ya fara aiki a NITT Zaria a 1994 sannan ya rike mukamai daban-daban.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng