Kano: An Kori Daraktoci 8 a Hukumar KIRS Mako Daya Bayan Kotun Koli Ta Mayarwa Abba Kujerarsa
- Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, tana ci gaba da sauye-sauye a hukumomin jihar bayan Kotun Koli ta tabbatar da shi a kan kujerarsa
- Hukumar tattara haraji ta jihar Kano wato KIRS ta sanar da tsige wasu daraktocinta guda takwas a ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu
- Shugaban hukumar, Sani Abdulkadir Dambo, ya bukaci daraktocin da abun ya shafa da su mika ragamar ayyukansu ga mataimakansu nan take
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Hukumar Tattara Haraji na cikin Gida ta Jihar Kano (KIRS) ta sanar da tsige wasu daraktoci guda takwas daga mukamansu, tare da umurtansu da su mika ragamar ayyuka ha mataimakansu.
Shugaban hukumar ta KIRS, Sani Abdulkadir Dambo, ne ya sanar da batun tsige su a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu, rahoton Kano Times.
Jaridar Daily Trust ta nakalto sanarwar na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Daga cikin kokarin da ake yi na cimma manufofin gwamnati mai ci, an umurce ni da na sanar da ku cewa an sauke daraktocin da aka ambata daga kujerunsu kuma za su mika shugabanci ga mataimakansu cikin gaggawa.”
Wannan ci gaban na zuwa ne mako guda bayan Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, tare da soke tsige shi da Kotun daukaka kara ta yi.
A ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu ne dai Kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara wacce ta tsige Gwamna Yusuf daga kujerarsa tare da tabbatar da shi a matsayin halastaccen gwamnan Kano.
Jerin sunayen daraktocin da aka sauke
- Muhammad Kabir Umar
- Kabiru Magaji
- Ibrahim Sammani
- Aminu Umar Kawu
- Muhd Auwal Abdullahi
- Abubakar Garba Yusuf
- Hamisu Ado Magaji
- Bashir Yusuf Madobi
Gwamnatin Kano za ta kashe biliyoyi kan ilimi
A wani labarin kum, mun ji cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware N8bn domin gina katafaran makarantun firamare a fadin jihar Kano.
New Telegraph ta ce wadannan makarantu za su samu kayan aiki da duk abubuwan da ake bukata domin neman ilmi.
Za a gina makarantun ne domin yara masu basira da suka fito daga gidajen marasa karfi domin gobensu tayi kyau.
Asali: Legit.ng