Satar Mutane a Abuja: “Mun Kama Wasu Masu Yiwa Yan Bindiga Leken Asiri”, Wike Ya Yi Karin Bayani

Satar Mutane a Abuja: “Mun Kama Wasu Masu Yiwa Yan Bindiga Leken Asiri”, Wike Ya Yi Karin Bayani

  • Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi karin bayani kan shirin da ake yi na dakile yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a babban birnin tarayyar kasar
  • A wata ganawa da shugaban karamar hukumar Gwagwalada da sauransu, Wike ya bayyana cewa an kama wasu mutane da ke yiwa yan bindiga leken asiri
  • Sai dai kuma, tsohon gwamnan na jihar Ribas bai bayyana adadin mutanen da aka kama ko karin bayani a kan kamun nasu ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce jami'an tsaro sun kama wasu mutane dake kaiwa yan ta'adda kwarmato da a babban birnin tarayyar kasar.

Ministan Abuja ya ce an kama masu yiwa yan bindiga leken asiri
Satar Mutane e Abuja: “Mun Kama Wasu Masu Yiwa Yan Bindiga Leken Asiti”, Wike Ya Yi Karin Bayani Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike ya ce wadannan mutane suna ci gaba da taimakon bata garin da bayanai a wuraren da ayyukan bata garin yayi kamari.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka farmaki wata jihar arewa, sun kashe sojoji da mutanen gari

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a Gwagwalada, tare da sarakunan gargajiya, jami'an tsaro, da mazauna yankin a Abuja, rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsaro zai kara inganta a Abuja, Wike

Duk da bai bayyana adadlin mutanen da aka kama ba, Wike ya bukaci mazauna yankin Gwagwalada da kada su tashi hankulansu yayin da ya ba su tabbacin cewa lamarin tsaro zai inganta a babban birnin nan da yan kwanaki, rahoton The Nation.

Wannan dai shi ne lokaci na biyu da ministan ya ziyarci yankin, tun bayan da lamurran tsaro suka kara kaimu a yankin.

Ministan ya kuma umarci kwamishinan yan sandan Abuja, akan ya samar da karin ofishin yan sanda guda biyu a yankin Gwagwalada.

Garkuwa da mutane don neman kudin fansa ya karu a wannan lokaci a birnin Abuja, lamarin dake kara haifar da damuwa a zukatan mazauna yankin.

Kara karanta wannan

"Abun kunya ne": Shugaban EFCC ya fallasa masu bincike da ke karbar na goro, ya bada sabon umurni

An kama madugun yan bindiga a Abuja

A wani labarin, mun ji cewa rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da kama wani mai suna Chinaza Phillip da ya shahara wajen garkuwa da mutane.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kama Phillip a jihar Kaduna yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano tare da masu taimaka masa da wanda suka sace, ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng