Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Kai Hari Ofishin Ƴan Sanda, Sun Tafka Barna Mai Muni Tare Da Kisa

Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Kai Hari Ofishin Ƴan Sanda, Sun Tafka Barna Mai Muni Tare Da Kisa

  • Yan bindiga sun kashe ɗan sanda ɗaya yayin da suka kai hari caji ofis a wani ƙauyen karamar hukumar Batsari a Katsina
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun yaudari jami'an yan sandan ta hanyar sanya Hijabi, sun far musu aka yi musayar wuta
  • Kakakin ƴan sanda ya bayyana cewa an samu nasarar dakile harin amma sun kashe mutum ɗaya, sun jikkata wani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wani jami'in rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ya rasa rayuwarsa yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari wurin da yake aiki a Batsari.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ƴan bindigan sun sanya Hijabi sun ɓoye fuskokinsu yayin da suka farmaki caji ofis a kauyen Saki Jiki da ke ƙaramar hukumar Batsari a Katsina.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sako ƙarin mazauna Abuja da suka yi garkuwa da su, sun turo saƙo

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan Bindiga Sun Halaka Jami'i Yayin da Suka Faramki Yan Sanda a Katsina Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Jumu'a, 19 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa baya da kashe ɗan sanda ɗaya, maharan sun kuma jikkata wani jami'i guda ɗaya a harin.

Yan sanda sun yi nasarar dakile harin

Ya ce lamarin ya faru ne da karfe 8 na daren ranar Alhamis, inda ya kara da cewa tuni ‘yan sanda suka ɗauki mataki kan lamarin.

A sanarwan da ya fitar, mai magana da yawun ƴan sandan ya ce:

"Jiya (Alhamis) da misalin karfe 8:00 na dare wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi suka kai hari a ofishin ƴan sanda dake kauyen Saki Jiki a karamar hukumar Batsari.
“Jami’an ƴan sanda sun mayar da martani cikin jarumtaka kuma sun yi nasarar dakile harin. Sai dai jami'i daya ya rasa ransa sannan wani ya samu rauni sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani 'Bam' ya tashi da mutane a jihar arewa, ya tafka mummunar ɓarna

"Zamu fitar da karin bayani idan bukatar hakan ta taso kan wannan hari nan gaba."

A baya-bayan nan ‘yan bindiga sun ƙara matsa kaimi wajen kai hare-hare a jihar Katsina, inda karamar hukumar Batsari kaɗai ta fuskanci hare-hare akalla biyu a mako.

Yan sanda sun kama hatsabibin ɗan garkuwa

A wani rahoton kuma Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Chinaza Phillip bayan musayar wuta.

Rahoto ya nuna dakarun ƴan sanda sun yi gumurzu da mayaƙan Phillip kafin daga bisa su yi nasarar kama shi da kubutar da wani mutum ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262