Bauchi: Yan Sanda Sun Sake Kama Dalibin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Da Bindigu a Gidansa
- Yan sanda a jihar Bauchi sun yi nasarar kama wani Mike James Habila, dalibin aji 4 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi
- SP Ahmed Wakil, mai magana da yawun rundunar yan sandan Bauchi ya ce an kama Habila ne bayan samun ingantattun bayanan sirri dangane da shi
- Kakakin yan sandan cikin sanarwar da ya fitar ya ce an samu wanda ake zargin da bindiga biyu kirar gida Najeriya da harsashi amma ya ce ba nasa bane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani dalibin aji 4 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa ta Bauchi (ATBU), Mike James Habila dauke da bindigu.
An kama shi ne a gidan zaman dalibai da ke kauyen Gubi a jihar ta Bauchi kamar yadda mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ya rahoto.
Kama Habila na zuwa ne bayan kama wani dan shekara 23 dan aji na uku duk dai a jami'ar ta ATBU da aka kama da irin wannan laifin a watan Disambar bara.
Kakakin yan sandan cikin sanarawar da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba ya ce binciken farko-farko da aka fara ya nuna wanda ake zargin ya mallaki bindigu kirar fistul na gargajiya biyu da harsashi mai tsawon 9mm.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama dalibin jami'ar da bindiga
An yi nasarar kwato makaman ne a ranar 13 ga watan Janairu yayin da tawagar yan sanda daga gudumar C karkashin jagorancin DPO, SP Abubakar Naziru Pindiga, suka kai samame bayan samun bayanan sirri kan James Habila.
A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa makaman ba nasa bane, mallakar wani Samson Irimiya ne wanda aka fi sani da Zaddeos, wanda a baya aka taba kama shi da fistul kirar gida Najeriya a Mayun 2021.
Sanarwar ta kara da cewa ana cigaba da bincike domin dakile dukkan laifuka masu alaka da wanzuwar muggan makamai a Bauchi.
Bidiyon Yadda Aka Kama Dalibi Dan Najeriya a Birtaniya Dauke da Tsabar Kudi $8.5m
A wani rahoton, wani bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da jami'an tsaron Birtaniya suka shiga gidan wani dalibi dan Najeriya, suka bankado wasu kudade masu yawa.
Rahotanni sun ce an kama dalibin ne da wasu daloli a cikin akwati, yawansu ya kai akalla $8.5m.
Asali: Legit.ng