Bayanai Sun Lalubo Biliyoyin da Tinubu Ya Kashe a Wajen Tafiye Tafiye a Watanni 6

Bayanai Sun Lalubo Biliyoyin da Tinubu Ya Kashe a Wajen Tafiye Tafiye a Watanni 6

  • Tafiye-tafiyen sabon shugaban Najeriya sun ci Naira biliyan 3.5 daga hawansa mulki a Mayun 2023
  • N2.49bn aka ware domin yawan da shugaban kasa zai yi, amma Bola Tinubu ya kashe fiye da haka
  • Tinubu ya ziyarci kasashe masu yawa saboda manufar inganta alaka, bunkasa tattalin arziki da zumunci

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya batar da akalla N3.4bn a wajen zirga-zirga a cikin gida da dogayen tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare.

A watannin da ya yi a ofis, Bola Ahmed Tinubu ya batar da fiye da kudin da aka ware domin tafiye-tafiye a kasafin shekarar da ta wuce.

Tinubu
Bola Tinubu a jirgi Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Kusan N3.5bn sun yi ciwo a yawace-yawacen Tinubu

Muhammadu Buhari ya sa hannu a kasafin kudin 2023 da nufin shugaban kasa zai kashe N2.49bn a kan tafiye-tafiye a shekarar bara.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan hawan Bola Tinubu mulki a karshen Mayu, an kashe karin 36% a kan abin da aka ware za a batar tun daga Junairu har Disamba.

Tinubu ya kashe kudi a sayen motoci da kudin abinci

Bayan tafiye-tafiye, sabon shugaban kasar ya amince a kashe N3bn wajen sayen motoci.

Rahoton da GovSpend ya fitar ya nuna N1.15bn aka kashe a tafiye-tafiye, amma wasu makudan kudin sun yi ciwo wajen biyan alawus.

Kudin Bola Tinubu ya kashe a kowane wata

A watan Yuni an fara da kashe N82.2m, sai aka batar da N393.3m a cikin Yuli, a Agusta da Satumba kuwa an kashe N393.3m da N287.9m.

GovSpend sun ce ba a kashe sisin kobo a Oktoba da sunan tafiya ba amma an ci N314m da N69.2m cikin watannin Nuwamba da Disamba.

Kamfanonin Hinterland Travels da Travel Options sun samu N732m wajen sayen tikitin jirgi saboda rage amfani da jirgin fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

An saye kudin kasar wajen N1.5bn

Wadannan tafiye-tafiye sun jawowa gwamnatin kasar kashe N1.53bn wajen sayen Daloli. Oluremi Tinubu kadai ta saye kudin waje na N77.7m.

Daga hawansa mulki zuwa yau, Tinubu ya ziyarci kasashen Turai, Larabawa, Afrika da na Asiya fiye da 10 haka mataimakin shugaban kasar.

Tawagar Tinubu a taron COP28

Ana da labarin yadda tafiyar shugaban Najeriyan zuwa wajen taron COP28 a Dubai ta jawo surutu saboda zargin an dauki mutane fiye da 1000.

Duk da fadar shugaban kasa ta ce mutum 422 kadai ta dauki nauyinsu zuwa kasar UAE, gwamnatin Najeriya ta kashe N2.78bn a tafiyar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng