Abin Da Ya Sa Muka Rufe Kantin Mu a Kano, Shoprite
- A ranar 14 ga watan Janairu, 2024 kamfanin 'Retail Supermarket Nigeria Limited (RNSL) ya sanar da rufe kantin Shoprite na Kano
- Shugaban kamfanin Hubertus Rick ya ce kamfanin ba ya kawo kudi duk da makudan kudaden da suka biya na tafiyar da shi
- A cewar Rick, tsadar kudin haya, rashin ciniki, kudin wutar lantarki da sauransu ya saka aka rufe kantin na Kano
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Kamfanin 'Retail Supermarket Nigeria Limited (RNSL)' dake aiki a matsayin 'Shoprite Nigeria' ya sanar da rufe babban kantinta na Ado Bayero da ke a jihar Kano.
Shoprite Nigeria ya fadi cewa biyan kudin wutan lantarki, tsadar kasuwanci, tsadar kudin haya da rashin kudaden shiga suka saka rufe kantin.
Da yake sanar da rufe kantin, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban kamfanin Hubertus Rick, ya bayyana cewa daga ranar 14 ga watan Janairu ne suka daina aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rashin ciniki ya saka aka rufe Shoprite na Kano
Tribune Online ta ruwaito cewa kamfanin zai ci gaba da rufe shagunan da ba kasuwancin ba ya kawo kudi yadda ya kamata, kuma za su bude sabbin kantuna hudu a duk shekara a fadin kasar.
Rick ya kuma ce daukar matakin bai zo da sauki ba, domin kamfanin ya fahimci irin wannan mataki zai yi tasiri ga ma'aikatan kantin da kuma al'umma.
Ya ce:
"Bayan yin la'akari game da shigar kuɗi na kantin da kuma yanayin kasuwanci na yanzu, Shoprite ya yi imanin cewa rufewa ne mafi alkairi don ci gaban kamfanin na dogon lokaci."
Abin da kamfanin zai yi wa ma'aikata kafin sallamarsu
Duk da hakan The Cable ta ruwaito Rick yana ba da tabbacin shirin kamfanin na yin kasuwanci a Kano idan yanayin kasuwanci ya ba da dama nan gaba.
Ko a baya bayan nan sai da Sanata Shehu Sani ya roki shugaba Tinubu da ya dakatar da kamfanin daga rufe kantin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa kamfanin zai taimaka wa ma’aikatan kamfanin dayanke hukuncin zai shafa, har zuwa sallamarsu baki daya.
Doka ta haramta yin lefe a jihar Kano
A wani labarin daga Kano, wani lauya Abba Hikima ya ce har yanzu akwai dokar da ta haramta yin kayan lefe da kayan daki a jihar Kano.
Abba Hikima ya ce idan aka kama mutum ya aikata laifin da ya saba wa dokar, alkali na iya cin tararsa ko ya daure shi, ko kuma a hada masa duka biyun.
Asali: Legit.ng