Gwamnatin Tarayya Ta Sake Shigar da Sababbin Tuhume-Tuhume Kan Emefiele, Bayanai Sun Fito
- An saurari ƙarar dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a babbar kotun birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu
- Gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi gyara a tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan na CBN
- An gyara tuhume-tuhumen zuwa 20, daga guda shida, wanda hakan ke nufin cewa matsalar Emefiele za ta daɗe ba ta ƙare ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sake yin gyara a tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.
Sabbin tuhume-tuhumen sun haɗa da amfani da takardun jaɓu, bayar da cin hanci da rashawa, da kuma cin amana da sauransu, cewar rahoton The Punch.
Tun da farko dai gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume 19 a kan tsohon gwamnan babban bankin na CBN kan badaƙalar kwangilar sayo kayayyaki amma daga baya ta ragesu zuwa shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a zaman kotun na yau Alhamis, 18 ga watan Janairu, lauyan gwamnatin tarayya Oyedepo ya shaida wa kotun cewa sun sake shigar da tuhume-tuhume 20 a kan Emefiele.
Da yake mayar da martani, lauyan wanda ake kara, Matthew Burkaa (SAN), ya shaidawa kotun cewa yana bukatar lokaci domin nazarin sabuwar takardar tuhumar.
Daga bisani mai shari’a Muazu ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar Juma’a.
Kotu ta amince da buƙatar Emefiele
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da buƙatar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ta neman a sassauta masa belinsa.
Kotun ta yarje masa cewa zai iya yin tafiya zuwa wajen Abuja, tare da gindaya masa sharaɗin cewa ba zai bar ƙasar nan ba.
Buhari Ya Bayyana Dalilin Ƙin Korar Emefiele
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya fito ya faɗi dalilinsa na ƙin korar tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Buhari ya bayyana cewa bai kori Emefiele ba ne saboda korarsa za ta zama zalunci ne da rashin adalci.
Asali: Legit.ng