“Na Fasa Kada a Raba Auren Ina Sonsa”, Matar da Ta Maka Mijinta a Kotu Ta Yi Amai Ta Lashe

“Na Fasa Kada a Raba Auren Ina Sonsa”, Matar da Ta Maka Mijinta a Kotu Ta Yi Amai Ta Lashe

  • Wata matar aure mai suna Sa'adatu Ayuba ta yi amai ta lashe a gaban kotu bayan ta nemi a raba aurensu da mijinta na shekaru 27
  • Sa'adatu dai ta zargi mijinta, Jalije da kin sauke hakkokin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na mai gidanta tun bayan da ya fara mu'amala da wata mata
  • Sai dai kuma, daga bisani ta nemi alkalin ya janye wannan batu na neman saki da ta zo masa da ita, cewa har yanzu tana son mijin nata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Wani abu mai kama da al'mara ya faru a ranar Laraba, a wata Kotu dake yankin Dei Dei a Abuja, bayan da wata matar aure ta roki kotu kan tayi watsi da bukatar da ta kai ta gaban mai shari'a.

Kara karanta wannan

"Wani ya dauka yace ta mutu": Budurwa ta koka yayin da 'yar uwarta ta bata bayan barin makaranta

Matar mai suna Sa'adatu Ayuba ta roki kotu akan kada ta amince da bukatar farko da taje da ita gabanta ta neman sakin aure.

Matar da ta yi karar mijinta ta ce har yanzu tana sonsa
“Na Fasa Kada a Raba Auren Ina Sonsa”, Matar da Ta Maka Mijinta a Kotu Ta Yi Amai Ta Lashe Hoto: Thisday
Asali: Twitter

Mai shigar da karar, wacce ta nemi a sauwake mata tun da farko kan hujjar rashin biya mata bukata, ta ce ta auri Jalija shekaru 27 da suka shige, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sa'adatu ta ce:

"Ya mai Shari'a duk da mijina ya gaza bin umurnin kotu na sauke nauyinsa a matsayinsa na mai gida, amma har yanzu ina sonsa."

Da yake martani, Jalija ya ce:

"Mai gidan da nake haya ya ba mu takardar tashi, don haka sai ta bar gidanmu. Na fada mata Ina so mu koma Dakwa saboda zarya zuwa wajen aikina, amma ta karbi hayar gidanta sannan ta koma a ranar 31 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Kano: Doka ta haramta yin lefe da kayan daki, abubuwan da ya kamata ku sani

"Tun da ta fada ma kotun cewa bana iya sauke hakkokina a matsayin miji, ya kamata kotun ta amsa rokonta. Na daina sonta."

Menene matsayin alkali a kan shari'ar?

Alkalin kotun mai Shari'a Saminu Sulaiman ya bai wa Jalija umarnin daukar matarsa zuwa inda yake zaune, tare da ɗaukar nauyin ta.

Mai shari'ar ya kuma umarci jami'in dan sandan kotun, akan ya raka ma'auratan har zuwa gidan su, tare da tabbatar da sun zauna a ciki.

Daga nan sai alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan nan na Junairu.

Mai karar ta tunkari kotu tun da farko don neman a saketa, cewa mijin ya daina biya mata bukata tun bayan da ya fara mu'amala da wata can daban, rahoton Daily Post.

Miji ya zargi suruki da kashe masa aure

A wani labari na daban, wani lamari mai sarkakiya ya faru a jihar Kano, inda wani malamin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya koka tare da zargin surukinsa da kashe masa aure.

Wasu takarfun gayyatar kotu sun bayyana bukatar ganin mijin, Aliyu Abdulrahman Aliyu a gaban kotun shari’ar Muslunci don tattauna abin da matarsa Amana Jaafar Muhammad ta gabatar na neman a tsinke igiyar aurensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng