Sauki Ya Zo Bayan Tinubu Ya Amince da Manyan Kudurori 3 da Za Su Sauya Rayuwar Talaka a Yau
- Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan wasu manyan kudurori da za su kawo sauyi a bangaren lafiya
- Shugaban ya dauki matakin ne a yau Laraba 17 ga watan Janairu a yayin taron majalisar zartarwa a Abuja
- Hausa Legit ta ji ta bakin wani mai harkar kasuwar magani inda ya yi martani kan lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya amince da wasu matakai don rage yawan tsadar magani a Najeriya.
Tinubu ya dauki matakin ne a yau Laraba 17 ga watan Janairu a yayin taron majalisar zartarwa a Abuja, cewar The Nation.
Wasu matakai Tinubu ya dauka kan magani?
Matakin da Tinubu ya dauka zai rage tsadar magani da kuma inganta harkokin lafiya da walwalar jama’a a bangaren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate shi ya bayyana haka ga manema labarai bayan taron farko na majalisar a 2024.
Pate ya ce matakan sun hada da rage hauhawan farashin magani da inganta bangaren da kudade da kuma dakile yawan fita kasashen waje ga ma’aikatan lafiya.
Farfesan ya ce wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren shugaban na inganta bangaren wurin samar da ma’aikata da kuma walwala a bangaren lafiya.
Mene fa'idar daukar matakan na Tinubu?
Ya ce wannan mataki ya zama dole ganin yadda manyan kamfanonin magani ke barin kasar wanda ke dakile gasa a tsakani, Within Nigeria ta tattaro.
Ya ce:
“Don samun daidaito da tsare-tsaren shugaban wanda ya fifita inganta bangaren lafiya ga ‘yan Najeriya.
“A yau yayin taron majalisar zartarwa, shugaban ya amince da wasu kudurori wadanda za su kawo sauyi a bangaren lafiya.
“Na farko shi ne dakile hauhawan farashin magani da ya ke gagarar ‘yan kasar da inganta lafiyar mutane da kuma matsalar wadatattun ma’aikata.”
Legit Hausa ta tattauna da wani mai kasuwar magani, Abubakar Umar Usman
Abubakar ya ce wannan abin farin ciki ne sai dai akwai bukatar daukar wasu matakai ba iya wadannan ba.
Ya ce:
"Muna farin ciki da wannan kudurin na rage farashin magani amma fa matakan da ya dauka ba su isa ba saboda kaso 70 na tsadar maganin ya rataya ne akan kamfanoni da kuma 'yan kasuwa.
"Domin haka dole a duba lamarin kamfanoni ta hanyar biyan haraji da biyan wani kaso daga gwamnati don samar da daidaito a farashin."
Tinubu ya shirya rage farashin sukari
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya na shirin daukar mataki don karya farashin sukari a kasar.
Wannan na zuwa ne yayin da farashin ya yi tashin gwauron zabi da ya fi karfin talaka a Najeriya
Asali: Legit.ng