Betta Edu: Kungiyar Arewa Ta Magantu Kan Shirin da Ke Alakanta Gbajabiamila da Rashawa

Betta Edu: Kungiyar Arewa Ta Magantu Kan Shirin da Ke Alakanta Gbajabiamila da Rashawa

  • Wata kungiyar arewa ta NEYGA ta yi martani kan shirin da ke alakanta shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da badakalar Betta Edu
  • Kakakin kunyiyar NEYGA, Ibrahim Dan-Musa, ya ce an kitsa lamarin ne domin mayar da tsohon kakakin majalisar wakilan abun dariya a wajen mutane
  • Dan-Musa ya ce nan ba da jimawa ba kungiyar arewar za ta fallasa mutanen da ke shiryawa Gbajabiamila manakisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Wata kungiyar Arewa ta NEYGA ta kare shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila yayin da ake zarginsa da hannu a badakalar dakataciyyar ministar jin kai, Betta Edu.

Mai magana da yawun NEYGA, Ibrahim Dan-Musa, ya ce masu son ganin bayan Gbajabiamila ne suke yi masa zagon kasa, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Tinubu, Shettima da gwamnoni sun dira Ibadan don taya Akande murnar cika shekera 85

Kungiyar arewa ta kare Gbajabiamila a badakalar Betta Edu
Betta Edu: Kungiyar Arewa Ta Magantu Kan Shirin da Ke Alakanta Gbajabiamila da Rashawa Hoto: @femigbaja/@edu_betta
Asali: Twitter

Dan-Musa ya ce an shirya zargin ne domin mayar da tsohon kakakin majalisar wakilan abun dariya a idon duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce wannan aiki ne da wasu daga cikin Villa da wajenta ke shiryawa, domin dai ganin an sauke Gbajabiamila tare da maye gurbinsa da su.

Ya kara da cewa duk masu hannu ko wadanda ke da masaniya kan wannan shirin aika-aikar, su kwana da sanin cewa sun makara domin kuwa hakan ba zai yi tasirin da suke tsammani ba, balle ya kai ga cikar burinsu.

Za mu fallasa masu yi wa Gbajabiamila zagon kasa, NEYGA

Idan za a tuna, a farkon makon nan ne aka fara ganin wata takarda tana yawo na amincewa da sakin kudi ga ma’aikatar jin kai.

Wannan takarda dai na dauke ne da sa hannun Gbajabiamila da kuma yawan kudin suka kai naira biliyan 3, kuma ake zargin an cire kudin ba tare da sanin shugaban kasa Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Betta: Gbajabiamila ya amince da N2bn ba tare da izinin Tinubu ba? Fadar shugaban kasa ta yi martani

Kungiyar ta yi alkawarin fallasa wadanda ke kokarin daure Gbajabiamila da binciken Betta Edu.

Daga nan sai suka yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan matakin gaggawa da ya dauka na dakatar da Betta Edu daga bakin aiki, tare da bayar da umarnin ci gaba da bincike kan zarge zargen da suka yi kamari akan ta.

Fadar shugaban kasa ta magantu

A baya mun ji cewa kakakin shugaban kasa, Onanuga ya yi martani kan zargin da ake yi wa Gbajabiamila na sakin naira biliyan 3 ba tare da amincewar shugaban kasa,

Onanuga ya bukaci yan Najeriya da daure sannan su kara hakuri, yana mai gargadi kan hukuncin kafafen yada labarai.

Sannan kuma, sabanin zargin da ake yi, Onanuga ya tabbatar da cewar Shugaba Tinubu ya amince da sakin naira biliyan 3 don tantance rijistan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng