Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Ofishin Jami'an Tsaro, Sun Tafƙa Mummunar Ɓarna da Kisa
- Yan bindiga sun halaka mace yayin da suka kai mummunan hari ofishin jami'an tsaro ƴan banga a jihar Ebonyi ranar Talata
- Shugaban ƙaramar hukumar Ohaukwu, Mista Odono, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wannan ba shi ne na farko ba
- Ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan wacce ta rasa ranta a bakin aiki, rundunar ƴan banga da ɗaukacin al'ummar ƙaramar hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki kan ofishin rundunar ƴan banga a jihar Ebonyi jiya Talata, 16 ga watan Janairu, 2024.
Yayin harin, ƴan bindigan sun yi ajalin jami'ar tsaro mace guda ɗaya da ke aiki da ƴan bangan mai suna, Onwe Blessing Onana.
Rahoton The Nation ya tattaro cewa wani ɗan banga ɗaya ya ji rauni a harin na ofishin jami'an tsaron Ngboejeogu Central Security da ke kotun Ngbo a ƙaramar hukumar Ohaukwu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ciyaman ya faɗi yadda lamarin ya faru
Shugaban karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi, Odono Onwe, ya tabbatar da kai sabon harin, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Ya ce harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro ɗaya, wani daya ya ji rauni, yayin da maharan suka yi awon gaba da wasu kadarori da babur
Odono ya yi nuni da cewa sau da dama wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sha duka, cin mutunci, zagi da kuma kisan wulaƙanci kan jami’an tsaro a karamar hukumar.
Ciyaman ɗin ya ƙara da cewa hare-haren na ci gaba da dagula lamurra da kokarin ’yan banga wajen kare yankunan da tabbatar da tsaro.
A kalamansa ya ce:
"Cikin alhini, muna miƙa sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan jami’ar tsaron da ta rasa ranta a bakin aiki, wanda ya ji rauni, jami’an tsaron Ngboejeogu Central Security, Ngboejeogu Clan, da daukacin al'ummar Ohaukwu.”
A cewarsa tuni jami’an tsaro suka ɗauki matakan ganin an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Yan bindiga sun nemi fansar shugaban ƙaramar hukuma
A wani rahoton kuma Yan bindiga da suka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Ukum a jihar Benue sun nemi kuɗin fansa kafin sako shi.
Wata majiya daga cikin dangi ta bayyana cewa maharan sun nemi N50m a matsayin fansar shugaban ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng