Yawancin hanyoyin Najeriya sun tashi aiki - FERMA

Yawancin hanyoyin Najeriya sun tashi aiki - FERMA

Hukumar kula da hanyoyi (FERMA) ta bayyana cewa yawancin hanyoyin Najeriya sun tashi daga aiki sannan kuma cewa kudaden da ake kashewa wajen gyara su ba zai wadatar ba.

Manajan Darakta na FERMA Injiniya Nurudeen Rafindadi ya fadama mambobin kwamitin majalisar dattawa na FERMA a lokacin ziyarar gani da ido a jiya a Abuja cewa yawancin hanyoyin Najeriya na da tsawon wa’adi na shekaru 20 amma sun wuce lokacin ba kadan ba.

Hakan na zuwa ne yayinda kwamitin karkashin jagorancin Sanata Magnus Abe (APC, Rivers), ya umurci FERMA da su ba da ka’idojin biya ga yan kwangila da suke aiki sannan su tabbatar sun yi yadda suke tsanmani.

Yawancin hanyoyin Najeriya sun tashi aiki - FERMA
Yawancin hanyoyin Najeriya sun tashi aiki - FERMA
Asali: UGC

Rafindadi yace: “Duk yadda kuka so ku kansu cikin kyakkyawar yanayi abu ne mai wahala. Don haka abunda gwamnatin yanzu ta mayar da hankali akai shine sabonta tsarin hanyarmu, sannan kuna iya ganin manufofin zuba jari daban-daban a shekaru uku da suka gabata. Abu ne mai wahala da baza’a iya magancewa cikin sauki ba."

KU KARANTA KUMA: Ku daina amfani da matasa a matsayin Karen farauta – Obasanjo ga yan siyasa

Ya kuma bukaci hukumar da ta gabatarwa da kwamitin rabe-rabe kudaden da suka saki daga 2017 ba tare da bata lokaci ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng