Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Babban Malamin Jami'a a Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Babban Malamin Jami'a a Jihar Arewa

  • Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da malamin jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi
  • Shugaban ASUU na jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumar makarantar ta kaɗu da abinda ya auku
  • Ya ce har yanzun masu garkuwan ba su kira iyalan malamin domin neman kuɗin fansa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da malamin jami'ar kimiyya da fasaha da ke Alieru, jihar Kebbi, Dakta Musa Sale Argungu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lakcaran da ƴan bindigan suka sace shi ne mataimakin shugaban "Faculty of Physical Sciences" na jami'ar.

Yan bindiga sun sace malamin jami'a a Kebbi.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malamin Jami'a a Jihar Kebbi Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU) reshen jihar Kebbi, Dakta Abubakar Birnin Yauri, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce an sace malamin da daddare.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan nasara a kotu, Gwamnatin Kano ta magantu kan masu niyyar wawushe asusun jihar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ƴan bindigan sun tare shi a hanya kana suka tilasta masa shiga motar da suka zo da ita, suka tafi da shi zuwa wani wuri da babu wanda ya sani ba.

Ya kara da cewa har yanzu hukumar jami’ar ba ta san inda malamin da aka sace yake ba kuma ba a sake jin ɗuriyarsa ba.

Ya ce:

"Abin takaici ne yadda a yau muka samu labarin sace malamin kuma mun kira taron dukkan mambobinmu domin tattauna yadda za a shawo kan lamarin."

Shin yan bindigan sun nemi kuɗin fansa?

Dangane da ko maharan sun nemi kudin fansa, ya ce har yanzu ba su kira iyalan malamin da aka sace don jin ta bakinsu ko neman kudin fansa ba.

Shugaban ASUU ya ƙara da cewa al'ummar jami'ar na cikin matukar kaduwa dangane da sace babban malamin da aka yi ba zato ba tsammani, inda ya yi addu'ar Allah ya kuɓutar da shi.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bai amsa kiran waya ko dawo da amsar sakonnin da aka tura masa ba har kawo yanzu.

An yi garkuwa da ɗaiban jami'ar Al-Qalam

A wani rahoton kuma miyagun ƴan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa bayan sun yi awon gaba da wasu ɗalibai mata guda biyu na jami'ar Al-Qalam da ke Katsina.

Ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne waɗanda suka fito daga jihar Neja a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262