Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Wata Yar Najeriya Ta Rasu a UK Jim Kadan Bayan Bikin Kammala Karatunta

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Wata Yar Najeriya Ta Rasu a UK Jim Kadan Bayan Bikin Kammala Karatunta

  • Oluwaseun Bello, wata matashiya yar Najeriya da ta kammala karatu a bangaren tsaron na'ura, ta kwanta dama
  • Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya sun tabbatar da faruwar al'amarin a cikin wata sanarwa da suka fitar
  • Kungiyar ta nemi tallafi daga jama'a a kan su taimaka da taro kwabo domin a samu a yi wa matar wacce ba a bayyana shekarunta ba jana'iza

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiya yar Najeriya wadda karatu ya kai ta kasar Burtaniya, ta kwanta dama inda ta yi sallama da duniya dungurungum.

Matashiyar Mai suna Oluwaseun Bello ta rasu ne yan awanni bayan an tashi taron taya ta murnar kammala karatun digiri a Burtaniya.

Yar Najeriya ta kwanta dama bayan kammala karatunta a Burtaniya
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Wata Yar Najeriya Ta Rasu a UK Jim Kadan Bayan Bikin Kammala Karatunta Hoto: @NIUKCommunity
Asali: Twitter

Alummar Najeriya mazauna Burtaniya sun yi alhini

Kara karanta wannan

Nasarawa: Fargaba yayin da matasan PDP suka aika muhimmin sako ga Kotun Koli gabannin yanke hukunci

Kungiyar alummar Najeriya mazauna Burtaniya ta tabbatar da labarin rasuwar Misis Bello, a cikin wata sanarwa da suka fitar domin nuna alhinin wannan abun ban al'ajabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa Misis Bello ta kammala karatunta ne a bangaren da ya shafi tsaron na'ura mai kwakwalwa, a jami'ar Bradford.

Sanarwar ta zo kamar haka:

"Zukatanmu sun yi nauyi yayin da muke alhinin rashin Oluwaseun Bello. Kwararriya ce a bangaren tsaron na'ura wacce ta kammala karatunta kwanan nan daga jami'ar Bradford.
"Ta rasu a ranar 1 ga watan Janairun 2024. A wannan mawuyacin lokaci da ake ciki, muna neman taimakonku domin daukewa yan uwanta nauyin binne ta. Gudunmawarku zai taimaka sosai. da fatan za a taimaka da abun da ya samu."

Limami ya rasu yana tsaka da sallah

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani al’amari mai taba zuciya ya auku a kasar Indonesia, inda wani limami ya rasu yana tsaka da sallah tare da mamu a wani masallaci.

Kara karanta wannan

APC ta sadaukar da kujerar gwamnan Kano ga Abba Kabir ne don gudun fitina? gaskiya ta fito

A bidiyon da Legit Hausa ta samo, an ga lokacin da limamin ya tada raka’a, har ta kai ga ya yi sujjuda, sujjadar karshe kenan a rayuwarsa.

A cewar Abdulfatah Ayofe, wani ma’abocin Twitter da ya yada bidiyon a shafinsa, lamarin ya auku ne a ranar 2 ga watan Janairun wannan shekarar da muka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng