Cikin Tsofaffin Gwamnoni Ya Dura Ruwa Yayin da EFCC Ta Shirya Sake Bincikarsu, An Bayyana Sunayensu
- Hukumar EFCC ta tana dab da sake buɗe wasu tsofaffin shari’o’in cin hanci da rashawa na wasu tsofaffin gwamnoni
- Majiya mai tushe daga hukumar EFCC ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sake bude shari’ar wasu tsofaffin gwamnoni
- Bayanai sun tabbatar da cewa wasu tsofaffin gwamnoni 11 ne ke kan sahun binciken EFCC, inda wasun su ke tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Yaƙi da cin hanci da rashawa da hukumar EFCC ke jagoranta da alama bai ƙare ba, inda aka sake mayar da hankali kan tsofaffin gwamnoni da ministocin da ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa.
A cewar wasu daga cikin jami’an hukumar ta EFCC, wasu tsofaffin gwamnoni sun fara shirin shari'a domin hukumar ta sanar musu da shirinta na bincikensu.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ƙuduri aniyar sake duba ƙararrakin da aka manta da su, ya kuma maido da masu bincike don ci gaba da gudanar da bincike da dama tun bayan hawansa mulki, cewar rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, tsofaffin gwamnonin da a halin yanzu ke fuskantar bincike sun haɗa da tsofaffin gwamnonin Enugu, Chimaroke Nnamani da Sullivan Chime, tsofaffin gwamnonin Ekiti, Kayode Fayemi da Ayo Fayose.
Sauran su ne tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan Gombe Danjuma Goje, tsohon gwamnan Sokoto Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido.
Zarge-zargen da EFCC ke yi wa tsofaffin gwamnonin
A Enugu, ana binciken Nnamani kan badaƙalar N5.3bn, Chime na fuskantar bincike kan zargin damfarar N450m na yaƙin neman zaɓe.
Waɗannan zarge-zargen dai na da nasaba da N23bn da ake zargin tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke ta raba, wacce ita kanta ake gudanar da bincike a kan zargin almundahanar kuɗaɗe.
Ana tuhumar tsohon Gwamna Fayemi kan badaƙalar N4bn, yayin da Fayose wanda ya gaje shi ke fuskantar bincike daga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kan badakalar N6.9bn.
A jihar Nasarawa ana binciken tsohon Gwamna Adamu kan badakalar N15bn.
A Abia dai ana binciken Orji Kalu kan zargin almundahanar kuɗi N551bn, kuma ana bincikarsa kan wata N7bn daban.
Hukumar ta na neman tsohon Gwamna Goje bisa zargin karkatar da N5bn, Wammako bisa zargin karkatar da N15bn, Sylva bisa zargin karkatar da N19.2bn, da kuma Lamido bisa zargin karkatar da N1.35bn.
EFCC Za Ta Waiwayi Binciken Matawalle
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya sha alwashin tado binciken tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle.
Matawalle wanda shi ne ƙaramin ministan tsaro ana zarginsa da yin sama da fɗi da N70bn lokacin da yake gwamnan Zamfara.
Asali: Legit.ng