Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Babbar Karamar Hukuma a Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Babbar Karamar Hukuma a Jihar Arewa

  • Ƴan bindiga sun aikata sabuwar ta'asa a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya a tarayyar Najeriya
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Ukum ta jihar, Haanongon Gideon tare da wasu mutum uku
  • Shugaban ƙaramar hukumar yana kan hanyarsa ne ta zuwa jana'izar Sarkin ƙaramar hukumar Katsina-Ala lokacin da aka sace shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga, da sanyin safiyar Asabar, sun yi garkuwa da shugaban riko na ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue, Haanongon Gideon, da wasu mutum uku.

Jaridar The Punch ta ce an yi garkuwa da shugaban ne a unguwar Anyagba, Tongov, cikin ƙaramar hukumar Katsina-Ala da misalin karfe 6:30 na safe.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta fara zaman shari'ar tsohon ministan da ake tuhuma da kwamushe dala biliyan 6

Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a Benue
Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma a Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

An ce an yi awon gaba da shi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa jana’izar babban sarkin ƙaramae hukumar Katsina-Ala, Ter Katsina-Ala, Cif Fezanga Wombo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka sace tare da shi har da mataimakinsa Mista Ior Yuhwam, direbansa, da ɗan sanda.

Yaushe aka sace shugaban ƙaramar hukumar?

Sai dai, wata sanarwar manema labarai da sakataren ƙaramar hukumar, Jonathan Modi ya fitar ta tabbatar da sace shugaban riƙon da wasu mutum uku, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Majalisar zartarwa ta ƙaramar hukumar Ukum na sanar da yin garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar, Rabaran Haanongon Gideon, tare da mai taimaka masa na musamman, Mista Ior Yuhwam, direbansa da jami’in ƴan sanda.
"Mummunan lamarin ya faru ne da safiyar yau, kusa da Anyagba, Tongov, a ƙaramar hukumar Katsina-Ala, ta jihar Benue, da misalin ƙarfe 6:30 na safe, a lokacin da yake kan hanyar zuwa jana’izar mai martaba Sarkin Katsina Ala, Ter Katsina-Ala, Cif Fezaanga Wombo."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar, Matthew Abo, shi ma ya tabbatar da sace shugaban ƙaramar hukumar.

A cewarsa:

"Gaskiya ne an sace shi, ba zan iya cewa komai ba a yanzu saboda ina wurin jana'iza a Katsina-Ala."

Ƴan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukuma

A wani labarin kuma, kun ji cewa Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukumar Ngeski a jihar Kebbi, Garba Hassan, tare da wasu mutane 12 a jihar Neja.

Hassan da sauran fasinjojin da ke cikin motar haya na kan titin Tegina zuwa Kontagora a jihar Neja da tsakar ranar lokacin da aka sace su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng