"Yan Najeriya Ba Su da Dalili 1 Na Zama Cikin Ƙangin Talauci" Shugaba Tinubu Ya Magantu
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa Najeriya da mutanen cikinta su zauna cikin talauci
- Shugaban ƙasar ya ce duk da karancin ababen more rayuwa, iimi da kiwon lafiya, ƙasar nan tana da albarka mai tarin yawa
- Ya bukaci gwamnonin APC da suka kai masa ziyara da su bullo da tsare-tsaren da zasu sauya rayuwar yan Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, ya ce ‘yan Najeriya ba su da wani dalili na zama cikin talauci, Channels tv ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin da aka zaɓa a inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Tinubu ya roƙi gwamnonin su tsara tare da aiwatar da manufofin masu kyau ga dukkan ‘yan Nijeriya kuma su duba maslahar kasa a koda yaushe sama da burikansu na siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Ba mu da dalilin zama matalauta. Idan muka duba inda muka fito, halin da muke ciki, dalilin da ya sa muke fama da ƙarancin ababen more rayuwa, da ilimi mara inganci, da karancin cibiyoyin kiwon lafiya, zamu ga ƙasar mu mai albarka ce."
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar an haƙaito Tinubu na cewa Najeriya ba gurɓatacciyar ƙaa bace, tana da albarka da tarin ni'ima.
Babban kalubalen da ake fuskanta a Najeriya
Ya shaida wa kungiyar gwamnonin APC (PGF) cewa daya daga cikin manyan kalubalen da al’umma ke fuskanta shi ne rarrabuwar kawuna.
Shugaban ya ƙara da cewa dole ne jam'iyya mai mulki ta himmatu wajen samar da waraka da hada kan kasa ta hanyar tabbatar manufa ɗaya da baki daya, da kuma gina ƙasa.
A cewar shugaban, manufofin kawo ci gaba za su samu matsuguni a rayuwar mutane ne kawai idan da haɗin kai mai da dorewa, rahoton Daily Trust.
Tinubu ya ce Allah ya yi wa Najeriya tarin albarka da albarkatun dan Adam, na halitta, da kayan aiki don ta yaƙi karancin kayayyakin more rayuwa, ingantaccen ilimi, da cibiyoyin kiwon lafiya.
APC ta yi magana kan nasarar gwamnonin adawa a kotun ƙoli
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta yabawa kotun koli bisa hukunce-hukuncen da ta yanke a ƙararrakin zaben gwamnonin da aka yi a watan Maris.
APC mai mulki ta bayyana cewa hukuncin da kotun kolin ta yanke ya ƙara nuna tabbacin cewa ɓangaren shari'a na cin gashin kansa.
Asali: Legit.ng