Bayan Nasarar Gwamna Abba, Rundunar Yan Sandan Kano Ta Bayar da Sabon Umarni
- Biyo bayan tabbatar da nasarar Gwamna Abba da kotun ƙoli ta yi, kwamishinan ƴan sandan Kano ya bayar da sabon umarni
- Kwamishinan ya umarci kwamamdojin shiyyoyi da DPOs da su ƙara zage damtse wajen gudanar da ayyukansu a yankunansu
- Umarnin na sa na zuwa ne bayan jami'an rundunar sun daƙile wasu ɓata gari da suka yi ƙoƙarin shigowa cikin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya umurci kwamandojin shiyyoyi da DPO na ƴan sanda da su ƙara zage damtse a yankunan da suke gudanar da ayyukansu.
Jaridar Vanguard ta ce umarnin na sa na zuwa ne biyo bayan yunƙurin da wasu ɓata-gari suka yi na shigowa Kano domin haifar da rikici.
Gumel ya ba da umarnin ne a ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai game da matsalar tsaro bayan hukuncin kotun ƙoli da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Yusuf, cewar rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa kwamishinan ya bayar da umarnin?
Ya ce umarnin ya zama dole domin wasu ɓata gari sun yi ƙoƙarin shiga Kano a cikin motocin bas da dama amma jami’an tsaron da ke wuraren shiga birnin suka hana su.
A kalamansa:
"Na buƙaci dukkan DPOs da sauran jami’an ƴan sanda da su ci gaba da sanya ido a wuraren da suke domin tabbatar da cewa jihar ta ci gaba da zama lafiya tare da kama duk wani mai shirin tayar da hankali ko kuma ya shigo jihar don tayar da hankali.
"Domin duk da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a jihar, wasu ɓata gari sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin Kano a cikin motocin bas da dama, amma jami’an mu sun hana su."
Ya ce dabarun da rundunar ta yi amfani da su sun taimaka musu matuka wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano kafin da lokacin da kotun koli ta yanke hukunci da kuma bayan yanke hukuncin.
A cewarsa:
"Tattaunawa da jama'a da kuma wa’azin zaman lafiya da ake yi a kai a kai ya taimaka sosai wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano."
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Abba
A baya rahoto ya zo cewa kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamnan jihar Kano.
Kotun ƙolin a hukuncin da ta yanke ta soke hukuncin kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara na soke nasarar gwamnan.
Asali: Legit.ng