Kano: Hotunan Yadda Abba Gida-Gida Ya Ke Murna Bayan Samun Nasara a Kotun Koli

Kano: Hotunan Yadda Abba Gida-Gida Ya Ke Murna Bayan Samun Nasara a Kotun Koli

  • Farin ciki ya lullube Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bayan da Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben sa
  • Kotun Daukaka Kara da kotun kararrakin zabe sun fara tsige Abba daga kujerar gwamna amma ya garzaya Kotun Koli
  • Legit ta ci karo da wasu hotuna da suka nuna gwamnan cike da farin ciki bayan da kotun ta tabbatar da shi ne gwamna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Juma'a 12 ga watan Janairu Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

A zaman da kotun ta yi, ta ce Kotun Daukaka Kara da kotun kararrakin zabe sun yi kuskuren korar Abba daga Gwamna.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda murna ta barke bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kano, bayanai sun fito

Abba Kabir ya samu nasara a Kotun Koli
Kano: Hotunan Abba Gida-Gida cike da farin ciki bayan samun nasara a Kotun Koli. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Hotunan Abba Gida-Gida a harabar Kotun Koli bayan nasara

Jim kadan bayan sanar da sakamakon, an hango gwamna Abba cike da farin ciki tare da mataimakin sa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga hotunan nan kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa a shafinta na Twitter.

Abba Kabir Yusuf a Kotun Koli
Kano: Hotunan Yadda Abba Gida-Gida Ya Ke Murna Bayan Samun Nasara a Kotun Koli. Hoto: LeadershipOnline
Asali: Twitter
Abba Kabir Yusuf a Kotun Koli
Kano: Hotunan Yadda Abba Gida-Gida Ya Ke Murna Bayan Samun Nasara a Kotun Koli. Hoto: LeadershipOnline
Asali: Twitter
Abba Kabir Yusuf a Kotun Koli
Kano: Hotunan Yadda Abba Gida-Gida Ya Ke Murna Bayan Samun Nasara a Kotun Koli. Hoto: LeadershipOnline
Asali: Twitter

Haka zalika, gwamnan ya yi hamdala a shafinsa na Twitter bayan jin hukuncin da kotun ta yanke.

Ga abin da gwamnan ya wallafa:

Kotun Koli na yanke hukuncin karshe kan zaben jihohi

Tun da farko dai, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Kotun Koli da ke zamanta a Abuja, ta saka ranar Juma'a 12 ga wata ta zamo ranar yanke hukunci kan zaben jihohi.

A safiyar ranar ne aka ga wasu gwamnoni tare da mataimakansu sun dira ginin Kotun Kolin don sauraron yadda shari'ar su za ta kasance.

Haka zalika mun ruwaito maku cewa akalla jihohi bakwai ne Kotun Kolin za ta yanke hukuncin zaben gwamnan su, ciki har da Kano, Legas, Plateau, Zamfara da sauran su.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci, ya gode wa wanda ya ba shi nasara

Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar Legas

Kotun Kolin ta fara karya kumallo ne da shari'ar gwamnan jihar Legas, inda ta tabbatar da Babajide Samwo-Olu matsayin wanda ya lashe zaben jihar.

Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar gwamnan Bauchi

A wani labarin kuma, Kotun Kolin ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed matsayin halastaccen gwamnan Bauchi tare da yin watsi da ƙarar da APC ta shigar.

Gwamna Bala dai ya yi nasara a Kotun lamarin da ya tabbatar da tazarcen sa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.