Dattawan Arewa Sun Yi Masifa a Kan Binciken da EFCC Tayi a Hedikwatar Dangote

Dattawan Arewa Sun Yi Masifa a Kan Binciken da EFCC Tayi a Hedikwatar Dangote

  • Kungiyar ACF ta yi Allah-wadai da binciken da EFCC ta je tana yi a ofisoshin kamfanin Dangote
  • Mai magana da yawun dattawan Arewa a jihar Kano, Bello Sani Galadanci, ya soki aikin hukumar
  • Alhaji Galadanci ya ce hakan ba zai jawo komai ba sai nakasa tattalin arziki da jawo rashin aikin yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Kungiyar ACF ta dattawan Arewacin Najeriya ta soki binciken da EFCC ta je tana yi a hedikwatar kamfanin Dangote.

Kungiyar dattawa Arewan ta ce hakan zai iya kawo matsalar tattalin arziki a Najeriya, Daily Trust ta fitar da wannan labari.

Dangote
Dangote da EFCC Hoto: Getty Images, EFCC
Asali: Getty Images

Sakataren yada labaran ACF na reshen jihar Kano, Bello Sani Galadanci, ya bayyana wannan da yake magana cikin makon nan.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun adawa sun cigaba da shirin hada kai domin yakar Tinubu da APC a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ACF ba ta ji dadin taba Dangote ba

Alhaji Bello Sani Galadanci ya ce abin da jami’an hukumar EFCC suka yi zai iya kora ‘yan kasuwa da ke shigowa da hannun jari.

Zuwa yanzu ana kukan ‘yan kasuwa ba su son kasuwanci a Najeriya, suna ta barin kasar.

Kakakin na kungiyar ACF ya kara da cewa abin da ya faru ba zai kawo cigaba ba, sai dai ya kara jawo tarbarbarewar tattalin arziki.

Dattawan Arewa sun yi tir da EFCC

Bello Galadanci ya kawo maganar wani ‘dan majalisar tarayya aka rahoto shi ya ce EFCC za su dada jagwalgwala halin da ake ciki.

A matsayin mai magana da yawun dattawan Arewa a Kano, Galadanci ya bada shawarar a maida hankali ne wajen bunkasa tattali.

Jaridar nan ta This Day a rahotonta, ta ce Galadanci yana so a samu hadin-kai ta yadda za a samu ayyukan yi a kasashen Afrika.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Gwamonin APC sun dauki mataki ana tsaka da binciken badakala, bayanai sun fito

Dangote: Maganar kakakin ACF

"Yanzu ba lokacin wannan ba ne; lokaci ne da kasa za ta maida hankali wajen hada-kan kasuwancin Afrika, a fadada ciniki da neman kudi a fadin nahiyar domin kawo cigaba, a samar da ayyukan yi, a maimakon kai samame a mafi girman kamfani."

- Bello Sani Galadanci

Harkar kasuwanci a Kano

Ministar kasuwanci a gwamnatin tarayya ta kai ziyara zuwa jihar Kano a ranar Alhamis dinnan kamar yadda labari ya gabata a Legit.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da manyan gwamnatinsa sun yi zama da Dr. Doris Anite domin ganin an iya bunkasa harkar kasuwanci a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng