Yan Bindiga Sun Bankawa Motar Kayan Amare 3 Wuta, Rayuka Sun Salwanta a Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Bankawa Motar Kayan Amare 3 Wuta, Rayuka Sun Salwanta a Jihar Arewa

  • Ƴan bindiga sun bankawa motar da ta ɗauko kayan ɗakin amare uku wuta, sun kashe direba da yaron motar a jihar Katsina
  • Ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru a kan titin Jibia zuwa Batsari ranar Talata lokacin da 'yan bindiga suka tare hanyar
  • Mutum ya ce an yi wa direban jana'iza amma ɗayan da suka tare ya kone ƙurmus ya zama toka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wasu mutane biyu da ake zargin direba ne da mataimakinsa sun mutu yayin da ‘yan bindiga dauke da AK-47 suka bude wa motarsu wuta a kan titin Jibia-Batsari a jihar Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a wani wuri da ake kira Sola a yankin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina kafin su ƙarisa karamar hukumar Batsari, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda.
Mutum 2 sun mutu yayin da yan bindiga suka bakawa motar kayan amarya wuta a Katsina Hoto: Dr Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

An ce motar ta taso ne daga kasuwar garin Ƴar Kasuwa da ke kwaryar birnin Katsina ɗauke da kayan ɗakin aure ta nufi wasu kauyuka da ke yankin Jibia da Batsari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya faru

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da ‘yan bindigan suka tare hanya, suka tare motar mai ɗauka da kayan ɗakin amare har uku.

A cewar wanda lamarin ya faru a kan idonsa, maharan ba su ɓata lokaci ba wajen ƙona motar mai ɗauke da kayayyakin da suka haɗa da gadaje, kujeru, da katifu guda huɗu.

Sai dai har yanzu hukumar ‘yan sanda ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin haɗa muku wannan rahoto.

Gaskiyar yadda maharan suka aikata ɗanyen aikin.

Wani ɗan jihar Katsina, Nasir Usman, ya shaida wa Legit Hausa cewa waɗanda lamarin ya faru da su duk yan unguwarsu ne kuma ya sansu farin sani.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama wani matashi saboda bankawa gidaje 4 wuta a Gombe, karin bayani sun fito

Usman ya bayyana sunan mutane biyu da ƴan bindigan da suka kashe da Awwalu da Abdullahi kuma a cewarsa suna da motar dakon kaya Hijert.

Ya ce:

"Anan cikin birnin Katsina a wata unguwa mai suna Sabuwar kasuwa ana siyar da kayan amare. Da maraice aka kira su ɗaukar wasu kaya zuwa Jibia amma aka ce su bari saida safe domin yamma ta yi."
"Da yake ajali ke kira suka ce a lokacin zasu tafi ai ba nisa, aka musu lodi amma ba su bi titin Jibia kai tsaye ba saboda yawan ma'aikatan da ke amsar na goro, suka bi hanyar Batsari."
"Suna cikin tafiya sai ga ƴan bindiga, Awwalu da ke tuƙi ya kone ƙurmus, shi kuma Abdullahi ya fito ya gudu amma duk da haka sai da suka harbe shi ya mutu."

A cewarsa, gawar Abdullahi kaɗai suka gani suka yi masa jana'iza amma Awwalu ya ƙone.

Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Yi Babban Rashi a Najeriya

Kara karanta wannan

Bayan kama 8, Asirin masu hannu a kisan bayin Allah sama da 150 ya ƙara tonuwa a arewa

A wani rahoton na daban kuma Allah ya yi wa yayar tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, rasuwa bayan fama da ƴar gejeruwar jinya a Bayelsa.

Madam Obebhatein Jonathan ta rasu ne tana da shekaru 70 a duniya ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262