Innalillahi: Yan bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 9

Innalillahi: Yan bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 9

  • An samu asarar rayukan bayin Allah bayan ƴan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a jihar Katsina
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai hari ne a ƙauyen Kukar Babangida na ƙaramar hukumar Jibia ta jihar
  • Mai unguwan ƙauyen da ɗansa na daga cikin waɗanda suka ransu a harin, yayin da ƴan bindiga suka kuma yi awon gaba da mata masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon farmaki a jihar Katsina inda suka halaka mai unguwa da ɗansa.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kukar Babangida da ke ƙaramar hukumar Jibia, inda suka halaka mai unguwan, Magaji Haruna da ɗansa, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

An bindige dan tsohon dan majalisar wakilan Najeriya a Amurka

Yan bindiga sun kai sabon hari a Katsina
Yan bindiga sun halaka mutum tara a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa wasu mutum takwas sun rasa rayukansu a harin wanda ya faru da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa:

"An kashe mutum uku tare da ɗan mai unguwar ƙauyen, Idris Haruna, waɗanda suke a gida ɗaya, yayin da mutum biyu kuma masu gadin wani kamfani ne mai suna Tinna Tech.
"Ƴan ta’addan sun yi wa ɗaya daga cikin masu gadin yankan rago sannan suka harbe ɗayan da bindiga.
"Sun kuma ƙona manyan motoci biyu na kamfanin da wata motar Golf guda ɗaya."

Wani majiya daga ƙauyen da ya tabbatar da labarin ya kuma ƙara da cewa an sace mata da ba a tantance adadinsu ba a yayin harin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin babban birnin jihar Arewa sun tafka ta'asa

Ya yi zargin cewa an gano shirin kawo harin tun da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Laraba lokacin da aka hangi ƴan ta’addan suna taruwa a ƙauyukan Taka-Tsaba da Yargeza.

Ya ce an sanar da jami’an tsaro amma abin takaici ba a yi wani abu da zai hana faruwar wannan mummunan lamari ba.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce mutum tara ne suka rasu.

Ya ce cikakkun bayanai sun yi ƙaranci game da harin amma ya yi alƙawarin ba da ƙarin bayani da zarar an samu.

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a yayin harin sun yi awon gaba da babban darakta a ma'aikatar kuɗi ta.jihar tare da iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng