Zo Ka Jaraba: Bature Na Neman Yan Najeriya da Za Su Iya Yin Minti 3 Suna Kuka, Zai Biya Daloli
- Wani mazaunin kasar Birtaniya yana neman duk wanda zai iya yin bidiyo na mintuna 3 yana kuka
- Wata matashiya da ta tallata damar ta ce mutumin abokinta ne kuma yana so ya yi amfani da shi a wakokinsa ne
- Ta bayyana yawan kudin da za a bai wa duk wanda ya yi da kuma wa'adin da aka dibarwa masu sha'awar abun don tura bidiyoyinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata matashiya yar Najeriya, Olaedo Chioma Irene, ta bayyana cewa wani abokinta a kasar Birtaniya yana bukatar wani da zai iya yin bidiyo mai tsawon mintuna uku yana kuka.
Ta ce mutumin na so ya yi amfani da bidiyon kukan ne a wakokinsa sannan ta bukaci duk wanda ke sha'awar abun ya tura bidiyonsa ta shafinta na WhatsApp.
Jerin Hukumomin Gwamnati Da Suka Bada Kyauta Ga Matar Da Ke Tashi 4.50 Na Asuba Don Yi Wa Mijinta Girki
Chioma ta bayyana cewa zai biya dala 100 (sama da N91k). Ta kuma jaddada cewar lallai kukan ya yi kamar gaske inda ta kara da cewar za a rufe gasar a ranar 15 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wallafar da ta yi a Facebook na cewa:
"Wani abokina a kasar Birtaniya, yana neman wanda zai iya yin bidiyon minti uku yana kuka.
"Ya yi kamar gaske, zai yi amfani da shi a wakokinsa (bangaren da ya bayyana wahalun da jama'a ke sha).
"Abokina ne a nan Facebook amma ba zan sanya sunansa ba.
"Idan za ka iya yin wannan kuma ya yi kamar gaske, ka yi magana.
"Za a biya dala 100.
"Kuna iya aika bidiyo zuwa lambar WhatsApp dina.
"Wannan bukata a bude take har zuwa ranar 15 ga watan Janairu."
Da aka tuntube ta don jin nau'in wakar da za a yi amfani da bidiyon kukan, Choma ta sanar da Legi cewa wakar Kirista ne.
Jama'a sun nuna ra'ayinsu
Uzor Prosper Chukwuma ya ce:
"Bari na je na nemi soja da zai mare ni."
Beatrice Patrick ta ce:
"Don Allah ina sha'awa sosai, ya yake son abun, shin akwai irin shigar da yake so mutum ya yi ne yayin daukar bidiyon kamar mai shan wahala....ya yake son abun ya kasance?"
Karolyne Ladii Joshua ta ce:
"Na ga waje.
"Hatta ciwon hakorin nan da nake ji na yi asarar kuka tun safe."
An taya filin matashi N80m
A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Joseph Okoro, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayyana cewa an yi masa tayin naira miliyan 80 a kan filin mahaifinsa.
Joseph ya ce mahaifinsa ya siya filin kan N250k a shekarar 2000.
Asali: Legit.ng