Babban Bankin CBN Ya Nada Shugabannin Bankuna 4 a Najeriya, Bayanai Sun Fito

Babban Bankin CBN Ya Nada Shugabannin Bankuna 4 a Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya naɗa sabbin shugabannin bankunan Polaris, Union da Keystone bayan korar tsofaffin shugabanni
  • Bankin na CBN ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa ta CBN, Sidi Hakama ta fitar da safiyar ranar Alhamis
  • A cewar sanarwar da daraktan ta fitar, naɗin sabbin shugabannin zai fara aiki ne nan take ba tare da ɓata lokaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sa'o'i kaɗan bayan rusa majalisar gudanarwar bankunan Polaris, Union, da Keystone, babban bankin Najeriya (CBN) ya naɗa sabbin daraktoci da za su kula da harkokin bankunan.

Babban bankin, a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan sadarwa na CBN, Sidi Hakama, ta fitar da safiyar Alhamis, ta ce naɗin ya fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Badakalar Betta Edu: EFCC ta kama shugabannin bankunan Zenith da Jaiz? Gaskiya ta bayyana

CBN ya nada sabbin shugabannin bankuna uku
Bayan korar shugabannin bankunan Union, Keystone da Polaris, CBN ya nada sabbi Hoto: CBN
Asali: UGC

Sanarwar ta ce, an naɗa Yetunde Oni, mace ta farko shugabar bankin Standard Chartered da ke ƙasar Saliyo a matsayin shugabar bankin Union, yayin da aka zabi Mannir Ubali Ringim a matsayin babban daraktan bankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, CBN ya naɗa Lawal Mudathir Omokayode Akintola a matsayin sabon manajan darakta kuma shugaban bankin Polaris da Chris Ofikulu a matsayin daraktan gudanarwa.

Su wanene sabbin shugabannin da CBN ya naɗa?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Bayan rusa majalisar gudanarwar bankunan Union, Keystone da Polaris a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, CBN ya naɗa sabbin shugabannin da za su riƙa kula da harkokin bankunan.
"Bankin Union: Yetunde Oni - Manajan darakta/shugaba, Mannir Ubali Ringim – Babban darakta.
"Bankin Keystone: Hassan Imam - Manajan darakta/shugaba, Chioma A. Mang - Babbar darakta.
"Bankin Polaris: Lawal Mudathir Omokayode Akintola - Manajan darakta/shugaba, Chris Onyeka Ofikulu - Babban darakta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada majalisar gudanarwa ta NAHCON, fitaccen malamin Kano ya shiga ciki

Sanarwar ta ƙara da cewa naɗe-naɗen na sun fara aiki nan take.

Idan dai za a iya tunawa a daren ranar Laraba ne babban bankin ya kori daukacin hukumar gudanarwar bankunan bisa wasu laifukan da suka saba wa dokoki.

Lemu Zai Yi Bayani Kan Alakar Emefiele Bankin Union

A wani labarin kuma kun ji cewa, babban mai bincike kan bankin CBN, Jim Obazee ya gayyaci Babatunde Lemu, shugaban bankin Titan Trust (TTƁ).

An gayyaci Lemu ne domin ya ba da bayani kan rawar da Emefiele ya taka wajen sayar da bankin Union.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng