Betta Edu: Kwanaki da Dakatar da Minista, An Gano Naira Biliyan 50 da ICPC Ta Bankado
- Hukumar ICPC ta hana a karkatar da wasu N50bn a lokacin da Muhammadu Buhari yake karagar mulki
- Sadiyar Umar-Farouk ce Ministar jin-kai a 2023 da aka nemi tura biliyoyi zuwa asusun wasu mutane a banki
- Farfesa Bolaji Owasanoye da ICPC sun dakile shirin, a karshe aka maida wadannan kudi cikin baitul-mali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
FCT, Abuja - Bayanai sun nuna binciken da ake yi a ma’aikatar jin-kai da yaki da talauci ya fara haifar da ‘da mai ido a Najeriya.
Rahoton da aka samu daga Punch ya tabbatar da jami’an hukumar ICPC sun gano kudi har N50bn a ma’aikatar jin-kai ta tarayya.
ICPC ta hana ayi gaba da N50bn
Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta tono wadannan makudan biliyoyi da ake shirin facaka da su ne a bara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsakanin watan Yuli zuwa Agustan shekarar 2023 aka bankado wadannan kudi, kuma yanzu an jefa su a asusun bankin CBN.
Jaridar ta ce an yi niyyar amfani da kudin da sunan taimakawa marasa galihu a lokacin da Sadiya Umar-Farouq tana minista.
...Lokacin Sadiya Umar-Farouq
An hana ministar tura kudin zuwa asusu a bankuna, a karshe ICPC a karkashin Farfesa Bolaji Owasanoye ta bankado shirin.
Wata majiya ta tabbatar da an mikawa gwamnatin Bola Tinubu wadannan N50bn bayan ya canji Mai girma Muhammadu Buhari.
Betta Edu za tayi koyi da Sadiya Umar-Farouq?
Bayan ta shiga ofis, Betta Edu bada umarnin tura N585m zuwa asusun mutane, irin laifin da ake zargin tsohuwar minista da aikatawa.
Akanta Janar ta kasa, Dr Oluwatoyin Madein ba ta bari ta tura wadannan kudi da sunan marasa galihu ba ganin hakan ya saba doka.
A dalilin haka aka dakatar da Betta Edu, kuma bayanai sun nuna binciken da ake yi ya shafi wasu jami’an da ke sauran ma’aikatun.
Yanzu haka hukumomi su na binciken Sadiya Farouk, Halima Shehu da kuma Betta Edu.
Binciken Sadiya Farouk da Betta Edu
Rahoton nan ya yi bayanin cewa Hukumar EFCC ta bigi ruwan cikin manyan jami'an hukumar jin kai, kuma ta samu muhimman bayanai.
Jami'ai 10 da aka titsiye har ana zargin sun fara fallasa irin badakalar da aka tafka a ma'aikatar da Muhammadu Buhari ya kafa a 2019.
Asali: Legit.ng