Badakalar Betta Edu: EFCC Ta Cafke Shugabannin Bankunan Zenith da Jaiz? Gaskiya Ta Bayyana
- Bankunan Jaiz da Zenith sun mayar da martani ga rahotannin cewa hukumar EFCC ta kama manyan daraktocin bankunan
- Labarin cafke manyan daraktocin bankunan dai yayi ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta bayan hukumar EFCC ta gayyace su
- Rahotanni sun ce dai manyan daraktocin na da alaƙa da binciken badaƙalar kuɗin da ake yi a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Bankin Zenith ya yi watsi da rahotannin da ke cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta cafke babban daraktan bankin, Ebenezer Onyeagwu.
Kamar yadda jaridar Business Day ta ruwaito, bankin Zenith ya ce labarin da aka samu game da kama Onyeagwu gaba ɗaya ƙarya ne.
Edu: Zenith ya musanta cafke babban darakta
A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu mai ɗauke da sa hannun Michael Otu, sakataren kamfanin, bankin Zenith ya yi watsi da labarin da ake yaɗawa ga jama’a game da kamun da aka yi wa Onyeagwu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi ta yaɗa cewa an cafke Onyeagwu ne dangane da binciken da ake yi kan zargin karkatar da kuɗaɗe a ma’aikatar jin ƙai da yaƙi talauci, ƙarƙashin Betta Edu wacce aka dakatar.
Wani ɓangare na sanarwar bankin na cewa:
"Hukumar EFCC ko wata hukumar yaƙi da cin hanci ba ta kama babban daraktan mu ba, kuma yanzu haka yana cigaba da gudanar da ayyukansa a bankin.
"Muna bayar da wannan sanarwar ga jama'a ne don kawar da bayanan ƙarya da kuma tabbatar da cewa jama'a da masu ruwa da tsaki sun san halin da ake ciki."
'EFCC ba ta kama shugaban mu ba' - Jaiz
Hakazalika, bankin Jaiz ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yadawa cewa hukumar EFCC, ta cafke babban daraktan bankin, Haruna Musa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A cewar bankin Jaiz, hukumar EFCC ta buƙaci wasu takardu ne kawai domin gudanar da bincike kan ayyukan ma’aikatar jin ƙai.
EFCC Ta Titsiye Shugabannin Bankunan 3
A baya kun samu labarin cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta titsiye shugabannin bankunan Providus, Jaiz da Zenith.
Hukumar dai tana yi wa shugabannin tambayoyi ne kan N44bn da aka gano an karkatar a ma'aikatar jin ƙai.
Asali: Legit.ng