Fitattun Yan Siyasar Kano 2 Sun Kwanta Dama, Abba Gida-Gida Ya Yi Alhinin Rashinsu

Fitattun Yan Siyasar Kano 2 Sun Kwanta Dama, Abba Gida-Gida Ya Yi Alhinin Rashinsu

  • Al'ummar jihar Kano sun yi babban rashi na wasu manyan jiga-jigai biyu a siyasar jihar, a kwanan nan
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alhinin wannan rashi, inda ya bayyana mamatan a matsayin wadanda suka yi fafutuka wajen kwato yancin al'ummarsu
  • Da yake mika ta'aziyya ga iyalinsu, Abba Gida-Gida ya roki Allah madaukakin sarki ya saka masu da aljannah madaukakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Shahararren dan siyasar jihar Kano, Alhaji Hamza Abdu Farar Hula Bichi, ya rasu.

Haka kuma, Allah ya dauki ran Alhaji Wada Sinkin wanda shima shahararren dan siyasa ne a jihar ta Kano.

Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rashin Alhaji Hula Bichi
Yanzun Nan: Fitaccen Dan Siyasar Kano Ya Kwanta Dama, Abba Gida-Gida Ya Yi Alhini Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Legit Hausa ta rahoto cewa Alhaji Hula Bichi fitacce ne a tsakanin yan siyasar Kano.

Kara karanta wannan

Ministan Abuja Wike ya yi kicibis da abokin karatunsa na sakanbdare, ya yi masa kyautar kudi a bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida-Gida ya yi alhinin rashin fitattun yan siyasar Kano, Hula Bichi da Wada Sinkin

Marigayi Hula Bichi ya kasance jigo a fafutukar kwato yancin al'umma a jihar ta Arewa maso Yammacin Najeriya.

Da yake martani kan mutuwar fitattun yan siyasar, gwamnan na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rubuta a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu:

“Ina mika ta’aziyya ga iyalan Alhaji Wada Sinkin da Alhaji Hamza Abdu Farar Hula Bichi kan rashinsu da aka yi a kwanan nan.
“Shahararrun ‘yan siyasan guda biyu sun yi fafutuka sosai wajen kwato ‘yancin al'ummarsu, kuma sun bar wani babban gibi da zai dauki lokaci mai tsawo kafin a cike shi.
"Allah madaukakin sarki ya saka musu da Jannatul Firdaus, Ameen."

Kara karanta wannan

Ana daf da yanke hukunci a Kano, Ganduje ya nemi alfarma daga 'yan adawa a jihar arewa

Babban malamin Musulunci ya rasu

A wani labarin kuma, mun ji cewa a a safiyar ranar Laraba ce aka samu labarin rasuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Kebbi.

Marigayi Sheikh Usman Abubakar Damana ya rasu a yau Laraba 3 ga watan Janairu a birnin Kebbi, cewar Dokin Karfe TV.

Kafin rasuwarshi, shi ne babban limamin masallacin Juma'an Geese Phase 1 da ke birnin Kebbi. Sshi ne mataimaki na biyu a kungiyar Izala a jihar Kebbi baki daya, cewar JIBWIS Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng