Jam'iyyar Adawa Ta Fadi Abu Mara Dadi da Za Ta Yi Wa Tinubu Idan Bai Dakatar da Ministansa Ba
- Jam’iyyar adawa ta Young Progressive Party (YPP), ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo
- Shugaban jam’iyyar YPP na ƙasa, Kwamared Emmanuel Bishop Amakiri, ya yi wannan kiran ne bisa alaƙar kamfanin Tunji-Ojo da Betta Edu
- Amakiri da jam’iyyarsa sun yi barazanar rufe Abuja idan har shugaba Tinubu ya ƙi dakatar da ministan na cikin gida
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja – Jam’iyyar adawa ta Youth Progressive Party (YPP), ta yi barazanar rufe Abuja idan har shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaza dakatar da ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Shugaban jam’iyyar YPP na ƙasa, Kwamared Emmanuel Bishop Amakiri, ya ce ya kamata a dakatar da Tunji-Ojo saboda “cin mutuncin ofis” da kuma bin ƙa’idojin da doka ta gindaya, cewar rahoton The Guardian.
Amakiri ya bayyana haka ne a wata wasiƙa da ya aikewa Shugaba Tinubu a lokacin da yake mayar da martani kan kwangilar da aka ba kamfanin New Planet Project Limited, wani kamfani da ake zargin Tunji-Ojo yana da hannun jari a ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci ƙarƙashin jagorancin Dr. Betta Edu ta biya kamfanin N438.1m domin aikin wata kwangila.
Meyasa YPP ke son Tinubu ya dakatar da Tunji-Ojo?
Ya ƙara da cewa biyan kudin na daga cikin N3bn da aka ware domin bayar da tallafi ga ƴan Najeriya masu rauni, rahoton Pulse.ng ya tabbatar.
"Yana da kyau a sani cewa kamfanin da aka yi wa rajista a ranar 3 ga watan Maris, 2009, mai lamba 804833, yana da minista Tunji Ojo da matarsa, Abimbola, a matsayin daraktoci, tare da Gbadamasi Gbadamasi Clement a matsayin sakataren kamfanin.
"Mun yi imanin cewa abin da minista Tunji Ojo ya yi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar ɗa’a.
"Sashi na 5 da 6 na dokar ƙa'idar aiki a fili ya haramtawa jami'an gwamnati amfani da matsayinsu domin cimma wani abu da shiga kowane irin kasuwanci banda noma."
Tinubu Ya Kira Tunji-Ojo Zuwa Villa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya kira ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo zuwa Villa.
Shugaban ƙasar ya gayyaci ministan ne bayan sunansa ya fito a badaƙalar kuɗi da ta shafi ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci, ƙarƙashin jagorancin Betta Edu.
Asali: Legit.ng