Tashin Hankali Bayan 'Yan Daba Sun Farmaki Sanatan Arewa a Gidan Gwamnati, an Kama Mutum 6
- Wasu 'yan saba sun kai farmaki kan Sanata Isah Echocho da ke wakiltar Kogi ta Gabas a jiya Talata 9 ga watan Janairu
- Gwamnatin jihar daga bisani ta sanar da cewa an cafke matasa guda shida kan zargin hannu a cikin harin
- Gwamna Yahaya Bello ya umurci hana mutane shiga Gidan Gwamnatin na tare da wani kwakkwaran dalili ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da kame wasu 'yan daba shida kan zargin kai hari kan Sanata a jihar.
Lamarin ya faru ne a jiya Talata 9 ga watan Janairu yayin da Sanatan ya kai wa gwamnan ziyara a gidan gwamnati, cewar Punch.
Mene dalilin kai harin kan Sanatan?
Sanatan da ke wakiltar Kogi ta Gabas, Isah Echocho ya bayyana yadda 'yan daban suka kai masa farmaki a Gidan Gwamnatin jihar da ke Lokoja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce 'yan dabar sun zabi ci masa mutunci shi kadai da zargin ya kawo cikas a nasarar APC a zaben da aka gudanar a mazabarshi.
Sanatan ya tabbatar da haka ne yayin hira da jaridar Daily Trust ta wayar tarho inda ya ce dukkan 'yan Majalisar Tarayya sun kai ziyarar ce don taya Gwamna Bello murnar nasarar zabe a jihar.
Martanin Gwamnatin jihar kan farmakin
Gwamna Yahaya Bello ya umurci hana mutane shiga Gidan Gwamnatin na tare da dalili ba inda ya bukaci a hukunta wadanda ake zargi da aikata laifin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Onogwu Mohammed ya fitar, cewar Kogi Reports.
Sanarwar ta ce:
"Bayan tattaunawa da 'yan Majalisun abubuwa masu muhimmanci, mun kadu da samun labarin kai musu farmaki yayin da suke kokarin fice wa daga Gidan Gwamnatin.
"Gwamna ya umarci jami'an tsaro su kama wadanda ake zargin tare da yin bincike don tabbatar da sun girbi abin da suka shuka."
Sanata Natasha ta yi rabo
A wani labarin, Sanata Akpoti-Uduaghan Natasha ta raba tirelar shinkafa 6 da wasu kayayyaki don bikin Kirsimeti.
Sanatar ta yi gargadin cewa wannan rabon na kowa da kowa ne ba tare da nuna bambancin addini ko siyasa ba.
Asali: Legit.ng