Fushin Allah Na Tare da Wadanda Ba Sa Biyan Haraji, Malaman Addini Sun Dira Kan 'Yan Najeriya

Fushin Allah Na Tare da Wadanda Ba Sa Biyan Haraji, Malaman Addini Sun Dira Kan 'Yan Najeriya

  • Malaman addinai sun gargadi 'yan Najeriya kan biyan haraji a kan lokaci ba tare da wata matsala ba
  • Alhaji Hamid Olanrewaju Wanda malamin addinin Musulunci ne ya shawarci ma'aikata su ji tsoron Allah bangaren biyan haraji
  • A martaninshi, Shahararren Fasto a Najeriya, Olusina Fape ya gargadi masu kin biyan haraji a kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Malamin addinin Musulunci, Alhaji Hamid Olanrewaju ya shawarci ma'aikata su ji tsoron Allah bangaren biyan haraji.

Hamid ya ce dole ne ko wane ma'aikaci ya cika alkawari kamar yadda gwamnati ta yarda da shi wurin biyan hakkin gwamnatin.

Malaman addini sun gargadi masu kin biyan kudin haraji a Najeriya
Malaman suka ce rashin biyan kudin haraji babban zunubi ne. Hoto: Pastor Olusina Fape.
Asali: Facebook

Mene malaman ke cewa kan biyan haraji?

Kara karanta wannan

Tashin hankali bayan 'yan daba sun farmaki Sanatan Arewa a Gidan Gwamnati, an kama mutum 6

A martaninshi, Shahararren Fasto a Najeriya, Olusina Fape ya gargadi masu kin biyan haraji a kasa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Olusina ya ce biyan haraji wajibi ne a addini inda ya ce wadanda suke kin biya sun saba umarnin Ubangiji.

Faston ya ce aikata hakan babban zunubi ne a wurin ubangiji wanda ya ke da girman gaske.

Malamin ya bayyana haka ne a Abeokuta da ke jihar Ogun yayin wata hudubar sabuwar shekara, Nigerian Bulletin ta tattaro.

Girman rashin biyan haraji a wurin ubangiji

Yayin da ya ke magana, Fasto Fape ya ce biyan haraji wani tsari ne na Ubangiji inda ya karanto ayoyi a cikin Injila da ke tabbatar da maganarsa.

Ya ce duk wadanda ba sa biyan haraji da masu cuwa-cuwa a karbar haraji duk matsayinsu daga a wurin ubangiji.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 13, Tinubu ya amince a biya iyalan sojojin da su ka mutu N18bn

A cewarsa:

"Dole ne a yi gaskiya a biya da kuma karbar haraji, wannan doka ce daga wurin Ubangiji.
"Duk wanda ba ya biyan haraji duk girmansa a cikin al'umma ya aikata mummunan zunubi a wurin ubangji."

Faston ya shawarci masu karbar haraji da su yi aikinsu tsakani da ubangiji don samun sakamako mai kyau a ranar kiyama.

Tinubu ya datse yawan kashe kudaden tafiye-tafiye

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya dauki matakin rage yawan kashe kudaden tafiye-tafiye ga mukarraban gwamnati.

Tinubu ya rage akalla kaso 60 daga yawan kashe kudaden inda ya ce zai shafi manyan masu mukamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.