Buhari ya lafta haraji a kan kayan waya, farashin yin waya ta salula zai tashi sama

Buhari ya lafta haraji a kan kayan waya, farashin yin waya ta salula zai tashi sama

  • Za a ga canji wajen kudin da ake kashewa a yayin yin waya ko aika sakonni daga salula
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta amince a kara haraji a kan wasu kayan
  • Jami’an kwastam za su karbi 5% a matsayin kudin shiga idan aka ci karo da kayan waya

Abuja - Kwanan nan masu amfani da wayar salula za su gamu da canjin farashin yin waya. The Cable ta fitar da wannan rahoto na musamman.

Za a gamu da karin kudi ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a rika karbar 5% a matsayin harajin da aka daura a kan katin waya.

A dokar tattalin arziki da aka shigo da ita a shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta amince a rika karbar kudin shiga daga irinsu katin yin kira a waya.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Ana cire wadannan kudi kan kayayyakin da aka kera da ayyuka a Najeriya. Gwamnati na karbar haraji kan sigari da giya domin rage masu kasuwa.

Wata takarda da fito daga hannun Ministar kudi da tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed, ta nuna kwastsam za su tatsi haraji kan wayoyin salula.

Zainab Ahmed ta ce doka ta yarda za a rika karbar kudi a wajen masu katin waya da wayar salula.

Buhari
Shugaba Buhari ya na waya Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Haka zalika jami’an kwastam za su biya karin kudi a kan na’urororin auna shan wutar lanyaki.

Rahoton ya ce gwamnatin tarayya ta na sa ran samun akalla N150b daga harajin, yayin da ma’aikatan kwasatam za su tashi 7% na kudin (N10bn)

Sashe na 21 (1) na dokar tattali ya ba jami’an gwamnati hurumin da za su yanke kudin da za a samu daga kayan da aka shigo da su ko aka yi su a nan.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun sheke na kusa da Shekau bayan yunkurin mika kansa ga sojoji

Shugaban kasa ne yake da hurumin da zai yanke kudin harajin da ke kan kayan wayoyi.

Kara haraji a kan kayan zai yi sanadiyyar da kamfonin sadarwa da ke kasar nan za su kara tsada. Daga ciki akwai kudin ROW, harajin shigowar kudi da VAT.

Fam ya yi tsada a PDP?

Okey Uzoho ya yi karar PDP a wani kotu da ke zama a garin Abuja a kan kudin sayen fam. Lauyan ya ce N40m da aka ware da sunan yankan fam, ya yi yawa.

Uzoho ya ce yana da sha’awar tsayawa takara a PDP a zaben 2003, amma an lafta farashin fam wanda hakan zai sa ba zai iya shiga zaben tsaida gwani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel