Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Garuruwa 3, Sun Kashe Rayuka da Yawa a Arewa
- Yan bindiga sun kai sabon mummunan hari kauyuka uku a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benuwai ranar Lahadi
- Rahoto ya nuna cewa maharan waɗanda ake zargin fulani ne sun halaka mutane bakwai a hare-haren da suka kai lokuta daban-daban
- Shugaban ƙaramar hukumar Logo, Adagbe Jonathan, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce 'yan sanda sun tsinto gawarwaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai a wasu kauyuka uku na karamar hukumar Logo a jihar Benuwai.
Rahotanni daga majiyoyi sun ce wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hare-haren a lokuta daban daban a ranar Lahadin da ta gabata.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, maharan sun far wa mutane a kauyukan Mchia, Arufu da Chembe da ke ƙarƙashin karamar hukumar Logo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shugaban al’ummar yankin, Joseph Anawa, ya bayyana cewa an yi kashe-kashen a Mchia ne da safe kuma an gano wasu gawarwaki yayin da wasu kuma suka bace.
Anawa ya ci gaba da cewa maharan sun kai hari na biyu ne cikin dare a tsakanin kauyukan Arufu da Chembe.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun harbi wata motar haya da ke kan hanyar zuwa Iorza inda fasinjojin suka samu raunuka daban-daban kuma yanzu haka suna asibiti a Anyiin.
Yan bindiga sun kashe mutum 7
Shugaban karamar hukumar Logo, Adagbe Jonathan, ya tabbatar da kai waɗannan hare-hare ga manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.
Ya ce ya zuwa yanzu dakarun ƴan sanda da mazauna yankunan sun gano gawarwaki bakwai daga cikin dazuzzuka, rahoton jaridar This Day.
Ciyaman ya ce an kai harin ne da karfe 9 na daren ranar Lahadi, kuma an gano gawarwaki biyar a cikin daren yayin da sauran biyun kuma aka gano su da safiyar ranar Litinin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Sewuese Anene, ba ta amsa kiran da aka yi mata ba da kuma sakon tes da ta aike mata ta wayar tarho.
Dakarun Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga
A wani rahoton na daban Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar sheƙe yan ta'adda 43 tare da kamo wasu sama da 100 a samame daban-daban cikin mako ɗaya.
Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce yanzu sojoji suna bin yan bindiga har cikin dajin da suke ɓuya, su halaka su.
Asali: Legit.ng