Betta Edu: Ministar Tinubu da Aka Dakatar Ta Mika Kanta Ga Hukumar EFCC

Betta Edu: Ministar Tinubu da Aka Dakatar Ta Mika Kanta Ga Hukumar EFCC

  • Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi mata jim kadan bayan dakatar da ita
  • Edu ta isa shelkwatar hukumar EFCC a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Janairu, kamar yadda rahotanni suka bayyana
  • Hukumar yaki da rashawar ta tabbatar da cewa Edu ta isa ofishinta da ke Abuja, inda ta ce ta fara tuhumar ta kan karkatar da N585.2

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa Betta Edu, ministar ayyukan jin kai da kawar da fatara da aka dakatar ta isa shelkwatar hukumar EFCC da ke Abuja.

Hukumar ta tabbatar da cewa Betta Edu ta isa ofishin ta, kuma har ta fara yi mata tambayoyi kan zargin karkatar da wasu miliyoyin naira ta hanyar ofishin ta.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: An wuce wurin, Hukumar EFCC ta dauki mataki kan ministar Buhari, ta fadi dalili

Ministar Tinubu ta mika kanta ga hukumar EFCC
Awanni bayan dakatar da ita, Ministar jin kai, Betta Edu ta mika kanta ga EFCC Hoto: @Edu_Betta
Asali: Twitter

Gidan talabijin na TVC News ne ya wallafa hakan, inda ya ruwaito cewa tsohuwar ministar ta isa ofishin safiyar ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunubu ya dakatar da Betta Edu kan karkatar da naira miliyan 585.2

A jiya Litinin ne Legit Hausa ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu.

Kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan inda ya ce shugaban ya dauki matakin ne don tabbatar da kudirinsa na bincikar duk wanda ya yi ba dai dai ba a gwamnatin sa.

Dakatar da Edu ya biyo bayan umarnin da Tinubu ya bayar na a gudanar da bincike kan yadda ministar da ba da izinin tura naira miliyan 585.2 zuwa wani asusu mallakin wani jami'i.

Kara karanta wannan

Jerin manyan mata yan siyasa 7 da aka zarga da cin hanci a Najeriya

EFCC ta dira kan Minista Betta Edu bayan dakatar da ita

Haka zalika, Legit Hausa ta a ruwaito maku cewa hukumar EFCC ta gayyaci Betta Edu zuwa ofishin ta da ke Abuja a ranar Litinin 8 ga watan Janairu, 2024.

Gayyatar na zuwa ne kasa da mintuna 30 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Edu daga mukaminta na ministan jin kai da kawar da fatara.

Wata majiya daga EFCC ta ce hukumar ce ta gabatar wa shugaban kasar bukatar dakatar da ministar don ba ta damar gudanar da bincike kan zargin karkatar da miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.