Badaƙalar N37bn: Jami'an EFCC Sun Titsiye Tsohuwar Ministar Buhari, Sun Tatsi Muhimman Bayanai

Badaƙalar N37bn: Jami'an EFCC Sun Titsiye Tsohuwar Ministar Buhari, Sun Tatsi Muhimman Bayanai

  • Hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta riƙe tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouk, ta kwana a hedkwata da ke Abuja
  • Wani jami'i ya bayyana cewa an samu ƙarin bayanai masu muhimmanci kan binciken da ake na ɓatan N37bn
  • Sadiya ta yi aiki ƙarƙashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma ta samu gayyata daga EFCC tun makon jiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) sun titsiye tsohuwar ministan jin ƙai, Sadiya Umar Farouk jiya Litinin.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, jami'an hukumar EFCC sun tasa Sadiya da tambayoyi domin tatsar bayanai kan badaƙalar wani kwantiragi da aka yi a ƙarƙashinta.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan babban banki CBN ya samu nasara kan Tinubu, kotu ta umarci a ba shi N100m

Tsohuwar ministar jin kai, Sadiya Farouk.
Jami'an EFCC Sun Titsiye Tsohuwar Ministar Buhari, Ta Kwana a Ofishinsu a Abuja Hoto: Sadiya Umar Farouk
Asali: Twitter

Tun farko hukumar ta tsara Sadiya Farouk zata kai kanta gaban jami'an EFCC da ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Laraba da ta gabata, amma ba ta je ba bisa dalilin rashin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohuwar ministar ta mika kanta domin bincike a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja da misalin karfe 10:00 na safe ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024, cewar Daily Post.

Sadiya ta kwashe sa'o'i shida tana amsa tambayoyi a kan badaƙalar biliyan N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar a ƙarƙashinta ta hannun ɗan kwangila, James Okwete.

Tsohuwar ministar ta kwana a hedkwatar EFCC

Da yake ƙarin haske kan lamarin, wani jami'in EFCC ya shaida wa jaridar cewa Sadiya Farouk zata kwana a ofishin hukumar domin su samu damar tattara bayanai daga bakinta.

Ya ce tsohuwar ministar ta basu haɗin kai, ta yi ƙarin bayani kan wasu takardu da ke hannun EFCC da kuma waɗanda ta zo da mu kamar yadda aka umarce ta.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Jami'in hukumar wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda ba shi da hurumin magana, ya ce:

"Tana bamu hadin kai sosai kan wannan bincike da muke yi kuma ta yi mana bayanai masu muhimmanci. Abin da zan iya faɗa muku shi ne mun tatsi bayanai game da ma'aikatar."

Duk wani yunƙuri na jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, bai kai ga nasara ba domin an kira wayarsa ta ƙi shiga.

Tsohuwar ministar, wacce ta yi aiki a karkashin tsohon shugaba Buhari, ta samu gayyata ne a makon da ya gabata daga hukumar EFCC bayan wani bincike da aka kaddamar kan ayyukanta a ma’aikatar.

Tinubu ya ƙara korar mutum 2 da Buhari ya naɗa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya kori wasu shugabannin hukumomi biyu waɗanɗa Muhammadu Buhari ya naɗa a lokacin mulkinsa.

Shugaban ƙasar ya basu umarnin miƙa ragamar jagoranci ga babban ma'aikacin da ke ƙasa da su nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262