Mata Sun Yi Zanga-Zanga Kan Kisan Wata Matar Aure da Mijinta Ya Yi a Yobe
- Kungiyoyin mata sun fito zanga-zanga kan kisan wata matar aure mai suna Ammi Adamu, a jihar Yobe
- An tattaro cewa ana zargin mijin Ammi da daba mata wuka a wuya yayin da take tsaka da bacci a gefensa
- Kungiyoyin matan sun sha alwashin bibiya da sanya ido har sai an kwatowa marigayar hakkinta na hukunta wanda ya aikata mata kisan gillar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Wasu kungiyoyin fara hula da mata ke jagoranta a jihar Yobe sun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Ammi Adamu Mamman, a garin Damaturu, jihar Yobe a safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, 2024.
Da take jawabi ga manema labarai a garin Damaturu, Barista Altine Ibrahim, shugabar kungiyoyin matan na jihar Yobe, ta ce an sanar da su faruwar mummunan al'amarin kuma sun shiga damuwa matuka kan bayanan da ke tattare da mutuwar Ammi Adamu.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Altine Ibrahim ta ce Ammi yar sa kai ce a daya daga cikin kungiyoyin matan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Altine Ibrahim ta ce:
"Yayin da muke sane da cewar tuni aka kama wanda ake zargi da aikata kisa, Abubakatr Musa, amma bayanan masu ban tausayi da tayar da hankali sun nuna cewa Ammi na bacci a gefen mijinta lokacin da aka kai mata hari tare da caccakarta da abu mai kaifi a wuya, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.
“Muna mika ta’aziyyarmu ga yan uwanta da masoyanta yayin da muke addu’ar Allah ya basu ikon jure wannan rashi, ya kuma kasance tare da su wajen nema mata hakkinta domin jinin Ammi ba zai kwaranya a banza ba."
Ya kamata a dunga ba mata kariya a gidajensu, Jagorar kungiyoyin mata
Ta ci gaba da cewa abun damuwa ne yadda kungiyoyin mata a jihar ke kokawa kan tsaron mata a gidajensu, cewa lallai akwai matsala idan har mace bata tsira ba yayin da take kwance da mijinta, wanda ake ganin shine kariya ga iyalin.
Ta yi kira da a yada wannan koken ta yadda za a yi wa tufkar hanci don gudun sake faruwar irin haka a gaba da kuma kare yancin mata cikin al'umma, rahoton PM News.
Daga karshe sun sha alwashin nemawa Ammi Adamu Mamman hakkinta daga wajen wanda ya aikata mata kisan gilla.
An kama magidanci kan kisan matarsa
A baya mun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama wani Abubakar Musa, bisa zargin sa da kashe matarsa, Ammi Mamman a garin Damaturu, jihar Yobe.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim, ya ce lamarin ya faru a ranar Alhamis, misalin karfe 4:48 na yamma.
Asali: Legit.ng