Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Yan Bindiga Suka Dawo Titin Kaduna-Abuja, Sun Sace Mutum 30

Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Yan Bindiga Suka Dawo Titin Kaduna-Abuja, Sun Sace Mutum 30

  • Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun dawo da ayyukansu a titin Kaduna zuwa Abuja
  • Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa abokansa guda biyu sun tsallake rijiya da baya a yayin harin yan bindigar
  • Duk da matakan tsaro da ke hanyar, mazauna yankin sun bayyana cewa yan bindigar sun toshe hanyar tare da aiki na kusan mintuna 45

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Yan bindiga sun farmaki matafiya a kan titin Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi, inda suka yi gakuwa da mutum sama da 30.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda abun ya afku a kan idanunsu da shugabannin yankin sun sanar da ita hakan a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Mata sun yi zanga-zanga kan kisan wata matar aure da mijinta ya yi a Yobe

Yan bindiga sun sace mutum 30 a hanyar Kaduna-Abuja
Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Yan Bindiga Suka Dawo Titin Kaduna-Abuja, Sun Sace Mutum 30 Hoto: Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

An yi garkuwa da mutanen ne a Dogon-Fili kusa da Katari, hanyar titin Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan shi ne karon farko cikin sama da watanni goma da aka yi kutse ga tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Bincike sun nuna cewa lamari irin haka da ya faru na karshe ya kasance a ranar 1 ga watan Maris, 2023, lokacin da aka yi garkuwa da mutum 23.

Yadda abokaina 2 suka tsallake rijiya da baya a harin, Shehu Sani

Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya tabbatar da harin a dandalinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), inda ya ce wasu abokansa biyu sun tsallake rijiya da baya a hannun yan bindigar.

Ya kuma bayyana cewa yan bindigar sun toshe hanyar sannan suka yi aiki na dan wani lokaci koda dai akwai jami'an tsaro a hanyar fiye da yadda ake da su a baya.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta mayar ta Dayyabu mijin Hafsat gidan yari bisa zargin kashe Nafiu

Sani ya ce abokan nasa biyu daga jami'iyyar adawa da mai mulki suna hanyarsu ta komawa Abuja daga Kaduna ne lokacin da suka tsallake rijiya da baya.

Sani ya ce:

"A daidai lokacin da muke ganin mun tsira, a daren jiya (Lahadi) masu garkuwa da mutane sun dawo hanyar Kaduna zuwa Abuja. Sun toshe hanyar sannan suka yi garkuwa da mutane da misalin karfe 9:00 na dare a kusa da kauyen Katari.
"Sai da abokaina biyu daga jam'iyya mai mulki da mai adawa suka yi gudu ta cikin jeji kamar motar tasi na Usain. Amma dai duk da wannan lamari, akwai cikakken tsaro a hanyar fiye da yadda ake da su a baya."

Martanin mazauna yankin da aka kai wa hari

Wani mazaunin Katari, Suleiman Dan Baba, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 9:33 na dare, lokacin da yan bindigar, rike da bindigogin AK-47 suka fito daga jeji sannan suka toshe hanyoyi biyun, yana mai cewa sun yi aiki na kusan mintuna 45.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake da wani manomi, sun tafka mummunar ɓarna a jihohin arewa 2

Ya kuma bayyana cewa yan bindigar sun bude wuta da fasa tayoyin wasu motoci, wanda ya tursasa direbobin, ciki harda motocin kasuwa tsayawa.

Wani mazaunin Jere, Samaila Shehu, ya ce lamarin ya faru ne a kimanin kilomita daya da Jere, kuma an yi awon gaba da matafiya sama da 30 a wurin.

'Yan bindiga sun raba kafa

Har ila yau, an rahoto cewa yan bindigar wadanda suka raba kan su gida biyu sun kuma kai farmaki a kauyukan Bishini da Kokore da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka kuma yi awon gaba da wasu mutanen kauyen da ba a san adadinsu ba.

Shuaibu Adamu Jere, wani shugaba a garin, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wasu danginsa sun tsallake rijiya da baya a kusa da Dogon Fili, kusa da garin Katari a ranar Lahadi.

Ya ce an raunata wani direba, sannan an gano wasu motoci biyu, motar Sharon da wata karamar mota, babu kowa ciki a gefen hanya bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bukaci naira miliyan 60 fansar yara 6 da suka sace a Abuja

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce zai bincike sannan ya gano abun da ya faru.

Yan bindiga sun farmaki al'ummar Abuja

A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidaje na 'Sagwari Layout' da ke yankin Dutse, babban birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi, kuma sun sace akalla mutum 10.

A cewar wani da lamarin ya faru kan idonsa, 'yan bindigar sun yi shigar kayan Fulani makiyaya, suka farmaki rukunin gidajen da misalin karfe 7:30 na yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng