EFCC Ta Fitar da Karin Bayani a Kan Binciken Daloli da Aka Yi a Babban Ofishin Dangote
- EFCC ta kare kan ta a sakamakon binciken da aka shiga yi a babban ofishin Dangote a garin Legas
- Hukumar yaki da rashin gaskiyar ta ce ta samu takardun da ta ke bukata daga hannun kamfanin
- Jami’an EFCC ba su da niyyar maidawa kamfanin martani, sun ce a saurari sakamakon binciken
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya ta yi karin haske game da ziyarar da jami’anta su ka kai ofishin Dangote.
Hukumar EFCC ta ce ba ta shiga kamfanin ba sai da ta samu izini da sahallewar doka, rahoton nan ya fito a jaridar The Nation.
Jawabin da hukumar ta fitar ya ce ana neman wasu muhimman takardu ne a kan yadda aka rabawa kamfanoni kudin waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya kai jami'an EFCC wajen Dangote?
EFCC ta ce binciken da ake yi ya shafi shekarun 2014 zuwa 2023 yayin da Mista Godwin Emefiele yake gwamna a bankin CBN.
Jami’an hukumar sun dura ofishin kamfanin Dangote Group ne saboda ma’aikatan ba su iya gabatar da takardun da aka nema ba.
A jawabin kamfanin, sun nuna sun ba hukuma hadin-kai wajen binciken da aka yi.
Rahoton ya ce jawabin ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu a ziyarar da aka kai a makon jiya domin ‘an samu abin da ake bukata’
Hukumar EFCC ba za ta tanka Dangote ba
Bugu da kari, hukumar yaki da rashin gaskiyar ta ce ba za ta biyewa kamfanin na Dangote ba, sai da jama’a su saurari bincikensu.
A na su bangaren, Dangote Group ya ce babu wani laifi da su ka aikata wajen harka da kudin kasashen waje a ‘yan shekarun nan.
Dangote da EFCC na musayar zance
EFCC ta ce babu wanda ya isa ya dakatar ko ya kawo cikas wajen binciken da ake yi, sai sun gano yadda CBN ya raba kudin kasar waje.
Kamfanin ya zargi jami’an da kokarin jawo masu abin kunya babu gaira babu dalili, kuma ba a dauki komai daga babban ofishinsu ba.
Matsayar kamfanin Dangote
An ji labEmari Dangote Group sun ga bukatar yi wa abokan huldarsu, masu ruwa da tsaki da sauran al’umma bayanin abin da ya auku.
Kamfanin ya ce an tura irin wannan wasikar da aka aiko masu zuwa ga sauran kamfanoni 51 ana bukatar bayanan nan daga gare su.
Asali: Legit.ng