"Dokar da TB Joshua Ya Bayar": Mutumin da Ya Yi Aiki a Cocin SCOAN Ya Fadi Yadda Ake Nadar Mu'ujiza

"Dokar da TB Joshua Ya Bayar": Mutumin da Ya Yi Aiki a Cocin SCOAN Ya Fadi Yadda Ake Nadar Mu'ujiza

  • Wani ɗan Najeriya, Paul Agomoh, ya ba da labarin yadda aka ce masu ɗaukar hoto su yi aiki a cocin TB Joshua
  • Mutumin ya ce marigayi TB Joshua ya ba su doka don ɗaukar duk wani abu da ke faruwa a cocin Synagogue Church of All Nations
  • Paul, wanda ya bayyana kansa a matsayin na kusa da TB Joshua, ya ce marigayin faston ya zo da wani abu na daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani jerin bincike mai kashi uku na BBC ya bayyana abubuwa da dama, inda wasu tsoffin mambobin cocin ke ba da labarin abin da ya faru a Cocin Synagogue of All Nations.

A wani ɓangare na faifan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wani tsohon na hannun daman marigayi Fasto TB Joshua ya ce an ba su umarni.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin masu mukamin da Tinubu ya nada kuma ya dakatar/cire su kasa da shekara 1

Na kusa da TB Joshua ya bayyana yadda ake daukar mu'ujiza
Mutumin ya ce TB Joshua ya umurci masu daukar hoto su dauki komai Hoto: YouTube/BBC African Eye/Twitter/TB Joshua.
Asali: UGC

Ya yi iƙirarin cewa faston ya saka sama da kashi 90% na duk kuɗin da aka samu wajen yin bidiyo na VHS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Kalamansa:

"Dokar da yake ba wa masu ɗaukar hoto ita ce "ku ɗauki komai". Bidiyoyi masu yawa, masu yawa sosai."

Ku kalli bidiyon a ƙasa:

Martani kan bidiyon mutumin da ya yi aiki tare da TB Joshua

@O_omayoza ya rubuta:

"Gaskiya kuna da ƙarfin hali fa. Mutumin da ba ya raye ta ya zai kare kansa, kuna dai son ci gaba da cin mutuncinsa."

@Callipers_ ya rubuta:

"Ɓangare na biyu ya kamata ya zama babban aikin. Yaushe zai fita don Allah?"

@Brighter6N ya rubuta:

"Ni da alama ni kaɗai ne wanda bai saurari wannan ba."

@OfficiaMichel55 ya rubuta:

"Me yasa basa magana lokacin yana raye? Lol bayan shekaru nawa. Za'a cika shekaru uku a watan Yuni lol."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara binciken minista kan badakalar N585.2m

@Femidaniels30 ya rubuta:

"Har yanzu ban san dalilin da yasa mutane ke ƙyamar wannan mutum ba, musamman wasu fastoci."

@Cynthia1_ibe ta rubuta:

"Ko da ya yi waɗannan duka, don Allah mutumin nan ya mutu. Su ƙyale shi ya huta."

Fasto Ya Yi Hasashen Rabewar Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Fasto David Kingleo Elijah, shugaban cocin Glorious Mount of Possibility, ya yi hasashen lokacin da Najeriya za ta rabe

Babban faston a hasashen na sa ya ce an gaya masa cewa kafin babban zaɓe mai zuwa Najeriya za ta zo ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng